Labarai

Shugaba Muhammad bubari Ya Nada Dr Bashar Aliyu Umar A Matsayin NCRI


Labarai Gwamnatin tarayya ta nada Dakta Aliyu Umar, a matsayin diraktan ma’aikatar binciken irin abinci na kasa da ke Badeggi, jihar Neja. Wannan labara ya samu ne a wasikar da diraktan harkokin jama’a na ma’aikatar noma da raya karkara, Mrs A. C Bawa a madadin ministan noma, Cif Audu Ogbeh. Wani sashen wasikar tace: 
Wannan nadi zai fara aiki ranan 2 ga watan Yuili kuma zai iya zama a kujerar har na tsawon shekaru 10 muddin baka isa shekarun ritaya ba bisa ga dokokin ma’aikatar.” 
An nada Dakta Aliyu Umar ne bayan mutuwan tsohon shugaban cibiyar, Dr Samuel Agboireso, a ranan 7 ga watan Yuni, 2018.

 An haifi Dakta Aliyu Umar a shekarar 1963 kuma ya fara aiki a ma’aikatar ne tun a matsayin karamin ma’aikaci har ya zama diraktan binciken waje. 

Ya rike kujeran shugaban reshen Uyo, Akwa Ibom da Amakama, jihar Abiya a shekarun baya. Ya samu kwalin doktoransa a ilimin kimiyar kasan noma daga jami’ar fasaha na Minna wato FUT Minna.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button