Addini

Ba Sheikh Daurawa ya fadi cewa abinda yafi muni a jikin mace ba shine (farji) Sayyadina Ali (RA) Ne – Prof Mansur Sokoto

Bayan karatun shehin malami ashsheikh Aminu Ibrahim Daurawa nacewa babu inda yafi muni da kazanta kamar gaban mace (farji) malam farfesa mansur Ibrahim sokoto ya kawo hujjar da cewa ba aminu Ibrahim daurwa bane kawai yayi fadi sonsa ba a’a ga abinda malamin ya wallafa a shafinsa.

Ba Sheikh Daurawa yadi cewa abinda yafi muni a jikin ba shine (farji) Sayyadina Ali (RA) - Prof Mansur Sokoto
Prof Mansur Ibrahim Sokoto

Ba Sheikh Daurawa ya fadi ba. Sayyidina Ali (RA) ne ya fadi. Ga maganar tasa kamar yadda Sheikh ya fade ta kwabo da kwabo:
قال علي لعمار: “لا تحزن على الدنيا فإنّ الدنيا ستة أشياء : مأكول ومشروب وملبوس ومشموم ومركوب ومنكوح ، فأحسن طعامها العسل وهو بزقة ذبابة ، وأكثر شرابها الماء ويستوي فيه جميع الحيوان ، وأفضل ملبوسها الديباج وهو نسج دودة ، وأفضل مشمومها المسك وهو دم فأرة ، وأفضل المركوب الفرس وعليها تقتل الرجال ، وأما المنكوح فهو النساء وهو مبال في مبال، والله إنّ المرأة لتزين أحسنها فيراد منها أقبحها”. انتهى
تفسير القرطبي – القرطبي – ج ١٧ – الصفحة ٢٥٥
Imamul Qurtubi a cikin tafairinsa (17/255) ya ce: Sayyidina Ali ya ce ma Ammar (RA): “Kada ka samu damuwa akan abin duniya domin jin dadin duniya abu shida ne kawai: Abin ci, da na sha, da na sa wa. Sai kuma abin shaka (turare/kamshi) da abin hawa da na aure. To, shi dai abincin duniya mafi dadinsa shi ne Zuma wacce fitsarin kuda ce. Mafi kyan abin sha ruwa ne wanda ko dabbobi shi suke sha. Tufafi kuma duk ba su kai darajar alhariri ba; sakar tsutsa ce. Kamshin turare kuma yana a bayan Miski; jinin wata bera ne. Abin hawa mafi daraja shi ne doki wanda a kan sa ake kisan maza. Aure kuma jin dadinsa yana wajen mata; wurin fitsari ne yake haduwa da wurin fitsari irin sa. Wallahi duk adon da ka ga macce ta yi, inda ya fi munin ne ake bukata (Farji)”.
Tafsirin Qurtubi (17/255).
Abin Lura:
Wa’azi akan a kiyayi duniya da kushe jin dadinta sanannen abu ne a cikin Alkur’ani da Hadisan Annabi (S) da maganganun magabatan Musulmi. Su kuma shakiyyan mutane neman wurin kushe Annabawa da karantarwarsu suke yi. Mai imani yana nisantar irin wannan tafarki nasu domin ya tsira da imaninsa.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

27 Comments

  1. Toh yan iska kake so su kare shi?
   Mas’ala ce ta ilmi kuma sune masu shi. A dinga tauna magana kafin a furta, pls.

  1. Toh yan iska kake so su kare shi?
   Mas’ala ce ta ilmi kuma sune masu shi. A dinga tauna magana kafin a furta, pls.

 1. To Allah ya kyauta amma gaskia maganar sayyadi Ali r a tasha bamban data daurawa domin shi Ali radiyallahu anhu cewa yayi gurin yafi muni a jikin mace shi ake bukata, shikuma daurawa idan ka fahimta kamar kushe abin yake da Nina cewa ba abune mai daraja ba kuma duk namijin da yake da iyali yasan yadda wurin nan yake kuma duk abubawan da ya fada kowa yasan anan suke fita a jikin mace nidai gaskia a fahimta ta ban tabbatar da sakon yake son ya isarwa al ummar musulmi ba anan

  1. Ya kamata ka nemi cikakken karatun kaji domin kayi wa kan ka adalci. Sai dai kuma idan kana da wata manufa toh wannan kuma daban.

  2. Gaskiya ya kamata kaji meye Asalin maganar malam. Daurawa baya magana akan Matan Aure ko ma’aurata.

 2. Shi ilimi fadi garesa kuma kowanne dan Adam da irin tasa fahimtar,Saidai muyi fatan cikawa da kyau da imani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button