Korar fatima: Dauda kahutu Rarara zai yiwa Fatima Mai zogale goma ta arziki
Bayan fitar wakar fatima mai zogale ta bayar baya da kura inda labarai nan fito cewa uwar gida Fatima mai zogale ta kori Hajiya Aisha ta kore ta daga wajen aiki.
Shine Hajiya Aisha ta fito a cikin wani faifan bidiyo da munka rahoto tana bayyanin cewa ita sam bata kore ta, tazo mata da maganar cewa aure zatayi shiyasa amma bata, taɓa korar wata yarinyar aikin ta ba.
Bayan kwana daya ita kuma Fatima mai zogale ta yi wani faifan bidiyo tana cewa wannan sam karya ne korar ta tayi saboda dalilin wakar da dauda kahutu Rarara yayiwa mata.
Bayan wannan chakwakiyya shine yanzu majiyarmu take samun labari daga wani fitaccen dan jarida Ibrahim sheme ya ruwaito cewa Dauda kahutu Rarara zai taimakawa fatima mao Zogale da jari domin itama ta kama tata sana’a kamar yadda ya bayyana cewa.
“Masha Allah, da alama Fatima Mai Zogale dai ta hau hanyar arziki. Shi ya sa aka ce wani hanin ga Allah baiwa ne.
Ɗazu mun gaisa da Dauda Rarara kuma na yi farin cikin jin cewa zai taimaka mata da jari ita ma ta kama sana’a. Har ya sa a nema mata wuri, zai biya. A gaskiya, ya kyauta.
Duk da yake ban faɗa masa ba, ni ma zan ɗan ba da tawa gudunmawar (ko ba yawa!) domin tallafa wa wannan baiwar Allah.
Dubun godiya ga Ciyaman Rarara wanda ta hanyar sa Allah ya tallafa wa Fatima. Da ma shi mai zuciyar yi ne, domin ya yi mun gani a wurare da dama.”