Labarai

Martani : Tabbas an kore ni a dalilin wakar Rarara – Fatima Mai Zogale

A yan kwana kin nan dauda kahutu rarara ya fitar da wakar mai zogale wanda nan take anka fara samun labarin cewa uwar gida Fatima mai zogala ta kore daga wajen aiki.

Wanda abun ya baiwa mutane mamaki da dama daga yiwa yarinya waka sai ki koreta , hausaloaded ta kawo muku wani gajeren bidiyo da hajiya Aisa take cewa ita ba korar fatima mai zogale tayi ba, aure tace zatayi shiyasa.

Yanzu kuma shine ita fatima mai zogale tayi magana inda take karyata uwar gida ta Hajiya aisha a cikin faifain bidiyo tana mai cewa.

“Dalilin da yasa na fito nayi magana shine naji uwar gida tana cewa nayi mata sheri bata kore ni ba , wannan shine karo na biyu da munka samu matsala da A’isha, a cikin azumi mun samu matsala da A’isha wani ya bani zanuwa guda biyu tace in bata guda daya ban bata ba, yace in dunka daya In bawa mahaifiyata ɗaya, shine dalilin da yasa munka samu matsala ta sallame ni a cikin azumi.

Bayan sati biyu da dawo wa Allah ya hadani da mawakin nan Rarara mai waka daman na dade ina dakon inda zanga rarara sai ranar shikenan bayan yan kwanaki kawai ankazo ankayimin hoto cewa za’a daura a wakar fatima mai zogale.

Bayan na tashi daga aiki sai naji ana fatima mai zogale sai hajiya aisha tace naji wakar fatima mai zogale kece da wuri ko nice, nace hajiya wannan cigaban da ni da ke ce saboda an daga darajar zogale, saboda alhamdullahi an samu kasuwar zolage tace waya umurce ni yin haka, nace wallahi ban san za’a yi haka ba, amma wannan abun cigaban mu ne ni da ke, daga nan ta juya bayimin magana ba.

Bayan Safiya na waye ta ce na sallame nace dan Allah kiyi hakuri sai na fara kuka, tace inyi hakuri fa komai zanyi ta sallame ni kenan daga wajenta tunda an min waka ba’a sanya sunata ba kuma itace mai zolage ni yarinyar mai aikice -inji Fatima mai zogale

Ga bidiyon nan ku saurara daga bakin fatima mai zolage.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button