Labarai

Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin Samar da aiki ga matasan Miliyan biyu kafin shekarar 2027

Ministar Al’adu da kirkire kirkire a Bangaren tattalin arziki Hannatu Musa
Musawa ce ta bayyana hakan a Taron karawa juna sani kan makamar aiki da
aka shiryawa ma’aikatan Maikatar ta a Abuja.

Tace an shirya kashe Euro Miliyan 100 ta hanyar kirkiro wasu masana’antu
a Najeriya kafin shekarar 2030.
Tace Zane Zane da Al’adu hanyoyi ne na Samar da aikinyi ga matasa a
Najeriya tana Mai cewa Maikatar ta zatayi amfani da umarnin Shugaban kasa
wajen Samar da aiki ga matasa Miliyan 2 kafin 2027.

Tace tun bayan kirkiro Maikatar da shugaban kasa Bola Tunubu yayi a
watan Augustan shekarar 2023 , Maikatar ta samu gagarumar nasara.

Wani labari : ‘Yan bindiga sun hallaka shugaban jam’iyyar APC a jihar Katsina

Wasu mahara da har lokacin hada wannan labarin ba a tabbatar da adadinsu ba, sun bindige Malam Sai’idu Jikan Basa wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC na mazabar Mai Dabino ta karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina.

Majiyar DCL Hausa ta tabbatar mata da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:37 na yammacin Larabar nan a kan hanyarsa daga Danmusa zuwa Mai Dabino.

Bayanai sun ce an kira jiga-jigan jam’iyyar APC na karamar hukumar Danmusa zuwa wani taro a hedikwatar karamar hukumar, inda daga kauyen Mai Dabino ya tafi Danmusa don halartar wannan taro.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button