Uncategorized

Wuff! Kyakkyawar likita yar Arewa Dr Halima Abubakar na neman mijin aure a Twitter

Wata likita daga yankin arewacin Najeriya ta je shafin soshiyal midiya don neman mijin aure, ta wallafa hotonta a shafinta na Twitter sannan ta tambayi mabiyanta ko suna bukatar matar aure.

Kamar yadda Legit na ruwaito,Dr. Halima Abubakar tare da shafin Twitter @DrHalima_ ta sa mabiyanta tattaunawa kan kyakkyawan hotonta wanda ta wallafa tare da rubutu kamar haka:
“Wa ke bukatar matar aure?”

Wani mai amfani da Twitter @AHMEDJEEKA ya rubuta:
“Ina ganin ba daidai bane tallata kanki a idon duniya kina neman abokan rayuwa, haramun ne a Musulunce. Mutum irina ina bukatar matar aure amma da irin wannan tallar, ina tsoro.”

@makoloumar1 ya wallafa:
“Shin za ki auri talaka mai kishin nema? + zan iya ciyar dake da baki kulawa sannan zan ba farin cikinki da kwanciyar hankalinki muhimmanci.”
@HerbertTruth ya yi martani da:

“Ina a hanyar zuwa gidan mahaifinki. Zan zo da magabata na yanzu haka. Babu lokaci.”
Ga sauran sharhin da aka yi:

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

13 Comments

  1. Allah ubangiji ya baki irin namijin da kike so, Wanda zai miki so kauna na gaskiya da hakika badan wani Abu ba, ya kyautata miki, ya faranta miki.

  2. Zan aureki Amma matana 1 yarana 4 kiyi hakuri ki aureni Zahara Tnx a lot for understanding my proposal Allah yasa inada rabo bye

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button