Kannywood

Sati mai zuwa jaruma khadija izzar so Khadija Yobe za’a daura aurenta da mawaki izzudden

Yanzu haka shirye-shiryen shagalin auren ‘yan masana’antar Kannywood biyu, ya kankama inda za a daura auren jaruma Khadija Yobe wacce aka fi sani da Karimar Izzar So da mawaki Izuddeen M. Doko. Shafin dimokuraɗiya na ruwaito

Jarumar ta samu karbuwa ne sakamakon shirin fim ɗin Izzar so mai dogon zamani wanda kowa ya santa.

Kuma ana matuƙar yaba mata kan yadda take shigar mutunci da kuma mu’amala mai kyau tare da abokan sana’arta. Sati mai zuwa jaruma khadija izzar so Khadija Yobe za'a daura aurenta da mawaki izudden

Kamar yadda Mujallar Fim ta bayyana an fitar da hotunan da masoyan suka yi kafin aure wanda mutane da dama suka dinga yi musu fatan alkhairi bayan ganinsu.

Za a daura auren ne a ranar Juma’a, 10 ga watan Fabrairun 2023 a daidai masallacin Juma’a da ke anguwar Nasarawa a garin Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.

Ana sa ran daurin auren na rana ne, don kamar yadda katin ya nuna, za a daura ne karfe 2 daidai. Allah ya sanya alkhairi kuma ya ba da ikon halarta, Amin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button