Ahmed Musa Da Abdullahi Shehu Sun Yi Wa Marayu Goma Ta Arziki A Sokoto Kalli hotuna
Ahmed ya ba su milyan daya, yayin da Abdullahi ya ba su buhunan shinkafa guda 100 da kayan masarufi
DAGA MUKHTAR HALIRU TAMBUWAL SOKOTO
‘Yan wasan kwallon kafar Nijeriya Ahmad Musa da Abdullahi Shehu sun kai ziyara a makarantar UK Jarma Academic (akasarin yaran daga jahohin maiduguri da Yobe wadanda suka rasa iyayen su sanadiyyar rikicin Boko Haram) inda Abdullahi ya ba su tallafin kayan abinci da suka hada da buhunan shinkafa guda dari, kwalin indomi hamsin da katon ashirin na lemun kwalba.
A bangaren wasanni kuma, Abdullahi Shehu ya b su kala biyu na kayan wasa da kwallo biyu domin su motsa jikinsu.
Dan kwallon na Nijeriya, Abdullahi Shehu dan asalin jihar Sokoto ne.
Abokinsa Ahmad Musa shi ma ya bayar da naira milyan da rabi domin cigaba da hidimar wadannan bayin Allah.
Shugaban hukumar zakka da wakafi na jiha kuma shugaban dauko yaran ne Malam Muhammad Lawal Maidoki ya karbe su a madadin Jarman Sokoto, Dr. Ummarun Kwabo.
A. A Kwamishinan Matasa da Wasanni ne ya jagoranci tafiyar matasan tare da goyon bayan dimbin matasa masu goyon bayan ‘yan wasan.