Babban goro sai magogin karfe :Sarkar gwal ta Naira miliyan 11 Hafsat Idris ta saka a sunan jikarta
Uwar mai jegon tayi fita ta kece raini da tsadajjen leshi mai dan karen kyau da sarkar gwal da aka yi kiyasin cewa kudin ta ya kai kimanin naira miliyan goma sha daya (N11m).
Kamar yadda labarunhausa sunka ruwaito, shafin labaran Kannywood dake dandalin Twitter ne ya tabbatar da hakan, inda suka wallffa hoton jarumar tare da rubuta:
“Sarkar gwal din da jaruma HAFSA IDRIS tasaka a ranar sunan jikar ta (Hafsa Jnr) ance kudin ta yakai Naira Milyan Goma Sha Daya!
“Allah ya kara arziki, Allah kuma ya raya mana Hafsa karama… Amin!
Sarkar gwal din da jaruma HAFSA IDRIS tasaka a ranar sunan jikar ta (Hafsa Jnr) ance kudin ta yakai Naira Milyan Goma Sha Daya!
Allah ya kara arziki, Allah kuma ya raya mana Hafsa karama… Amin! pic.twitter.com/USw7w0epA7— Labaran Kannywood (@Hausafilmsnews) February 1, 2022
Jarumai mata da dama sun halarci wannan gagarumin shagalin suna irin su Mansurah Isah, Sameera Ahmad, Aina’u Ade, Sadiya Gyale, da dai sauran su.
Ga kadan daga cikin bidiyon wajen bikin:
View this post on Instagram
One Comment