Dukda Gwamnatin Ku ta Haramta amma zamu taimaka maku kuci Gaba da shiga Twitter Kuna anfani da ita ~Inji Kwamfanin Twitter
kamfanin yada labarai na Microblogging na Twitter sun bayyana shirinsu na taimakawa ‘yan Najeriya samun damar shiga dandalin na Twitter duk da cewa gwamnatin Najeriya ta hana.
A cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, ministan sadarwa na Najeriya Lai Mohammed ya sanar da dakatarwar, dangane da wannan shawarar da kasar ta yanke, Twitter ta wallafa a shafinta na manufofin cewa za su yi aiki don dawo da damar ga dukkan ‘yan Nigeria, Kamar yadda jaridar mikiya na ruwaito.
Mun damu matuka da toshewar shafin Twitter a Najeriya. Samun dama kyauta na Shiga #OpenInternet hakki ne na ɗan adam a cikin zamantakewar zamani.
“Za mu yi aiki don dawo da dama ga duk wadanda ke Najeriya wadanda suka dogara da Twitter don sadarwa da cudanya da duniya. #KeepitOn, “kamfanin ya sanya wannan a yau ranar Asabar.