Labarin mahaifin mu da ya tara ‘certificate’ guba ɗari biyu da saba’in – Muhammad kiru
Wani matashin mai amfani da kafar sada zumunta ta Facebook mai suna Muhammad Ubale Kiru cikin ban tausai da kuka ya bada labarin irin tarin certificate din da mahaifinsa ya tara a duniya kafin ya komama mahalicinsa.
Ga yadda labarin ya kasance.
Wato wannan hoto ya saka ni kuka. Akwai dinbun darrusa a cikin wannan hoto. Duk sanda na bude jakar credentials dina na kalli yawan certificates dina. Sai nayi kwalla. Domin idan kana da lura zaka gane cewa duk takardun banza ne. Saboda idan ka mutu basu da wani amfani.
Bayan rasuwar mahaifin mu, ya bar certificate guda dari biyu da saba’in. Da yaje screening na election a 2007, Wallahi a akwati aka dauki credentials dinsa. Wallahi mamaki ne ya kama su a wajen screening din. Amma bayan rasuwar sa ina kuka ina kona su. Saboda basu da wani amfani. Wani baya gadar certificate din wani.


Gane hakan da nayi, shi yasa na dauki wasu matakai kamar haka:
1. Sharing ilimina ga duk wanda yake so. Rubuta littittafai, wallafa research, yin rubututtuka da zasu amfani al’umma da kuma koyar wa a makarantu, da bada lokaci na ga bloggers don koyar wa. Ni a tsari na, ban taba zama bama koyarwa ba. Duk inda na samu kaina sai na koyar. Ko aiki nake, sai nayi part time teaching. Sabida Manzon Allah SAW ya ce duk abinda ka koyar wa wani na ilimin ko ka mutu ladan zai ci gaba da samun ka. Ta haka ne kadai certificate zai maka amfani.
2. Bada kyautar littafi. Ni bana ado da books kamar yadda naga wasu su nayi. Duk books dima na degree da masters da leisure readings, tattarasu nake ina bayarwa. Ko three months ago nayi wa BUK library donating over 200 books. Sannan ina da virtual libraries across the internet da nake raba littittafai kyauta. Wai fa burina shine idan na mutu a ci gaba da amfanuwa da ilimi na da certificates dina.
3. Na gane cewa karatun addini shine kadai karatun da baka asarar sa a duniya. Certificate din ka da shi kake tafiya lahari. Kuma acan zai maka amfani. Don haka har yanzu ban daina karatun addini ba. Kuma ko na tsufa zan ci gaba. A haka ne kadai zan anfana da ilimin da certificate ya bani.
Don haka masu rowar ilimi ku sani, idan kun mutu shikenan. An rufe babin ku. Certificates din ku a kona. Books din ku a sayar ko a bayar. Is better ku bayar da kanki tun kana da iko don ku samu ladan kuma ku amfana da yin hakan ba sai ka mutu a ma rasa wanda za’a baiwa. Allah ya sa mu dace.
✍️Muhammad Ubale Kiru
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






