‘Yan Ta’adda Sun Kai Hari Garin Mahaifar Ministan Tsaro, Sun Yi Garkuwa Da Sama Da Mutane 50
Da sanyin safiyar Juma’a ne wasu gungun ‘yan ta’adda suka mamaye garin Maradun hedikwatar karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara inda suka yi garkuwa da mutane sama da 50 musamman mata.
Maradun shine mahaifar karamin ministan tsaro na Najeriya, Hon. Bello Muhammad Matawalle.
Wani mazaunin yankin mai suna Malam Sulaiman Maradun a wata tattaunawa ta wayar tarho ya shaida cewa ‘yan ta’addan sun yiwa garin kawanya da misalin karfe 12 na safe inda suka fara gudanar da ayyukan gida-gida.
“Abin takaici ne yadda suka afka garinmu saboda sun zo da wasu makamai masu kisa kuma suka fara harbe-harbe ta iska a tsakar daren yau Juma’a,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kashe mutane 10 tare da yin awon gaba da su har yanzu ba a tantance adadin dabbobin jama’ar yankin ba.
Ya ce ‘yan ta’addan sun kai hari a fadar Sarkin Maradun Alhaji Garba Tambari sai dai basu sami sarkin ba.
“Wannan ba shi ne karon farko da wadannan ‘yan ta’addan da ake fargabar ke kai wa al’ummar Maradun hari ba. Ya kamata gwamnati a dukkan matakai su dauki tsauraran matakai don magance matsalar rashin tsaro da ke addabar yankinmu.”
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da na jihar Zamfara da su kara tura dakaru zuwa yankin domin ceto jama’a daga munanan ayyukan ‘yan ta’adda da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.
A Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Asp Yazid Abubakar, ya ci tura, saboda ba a samu dukkan layukan sa ba har lokacin hada rahoton.
Rahmatv