Labarai

Murja kunya: Sheikh Daurawa Bai Yi Murabus Ba —Hukumar Hisba

Advertisment

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da cewa har yanzu Babban Kwamnadanta, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa na nan kan kujerarsa bai yi murabus ba.

Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah na Jihar, Sheikh Mujahid Aminuddeen Abubakar ne ya sanar da hakan.

Sheikh Mujahid ya bayyana haka ne bayan rade-radin da ke yawo cewa Sheikh Daurawa ya yi murabus, kan takaddamar sakin jarumar tiktok, Murja Ibrahim Kunya, daga gidan yari, bayan kotun Musulunci a ba da umarnin tsare ta.

A ranar Lahadi Aminiya ta ruwaito cewa an fitar da Murja daga gidan yari, sabanin umarnin kotu, lamarin da ya haifar da damua a cikin al’umma.jaridar Aminiya na ruwaito

Kotun Shari’ar Musulunci da ke Gama PRP a Jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare matashiyar a gidan yari ne ba bayan hukumar hisbah ta gurfanar da ita kan zargin karuwanci ga kananan yara,  da kuma badala, zargin da ta musantarbiyya.

Alkalin kotun, Mai sharia Nura Yusuf Ahmad, ya bayar da umarnin tasa keyarta zuwa gidan yari tare da dage shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Fabrairu, 2024.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button