Addini

Sakin Aure A Cikin Fim Har Matarsa Ta Gida Ta Saku ?~ Matsayar Sheikh Dahiru Bauchi

Advertisment

Daya Daga Babangida A Maina marubuta shafin darikar tijjaniya Fityatul Islam shine ya kawo wannan fatawar a matsayin babban shehinsu Sheikh Dahiru usman bauchi ida yake cewa.

Shahararren masanin Alkur’ani a fadin Afrika Sheikh Dahiru Usman Bauchi yayi bayani a wani audio akan fatawar hukuncin wanda ya saki matarsa a cikin shirin fim.

Shehin Malamin ya yi bayanin cewa: idan matar da yake fim din da ita matarsa ce har a zahiri sannan ya furta mata saki, ba makawa matar nan ta saku don ba’a wasa da saki. Idan kuma ba matarsa bace amma ya sake ta don kawai suna fim, hakan ba zai zama matarsa ta gida ta saku ba, saki bai hau kan matarsa ba don bai yi niyyar hakan akanta ba.

Wannan shi ne fatwan da malamin ya bayar akan sakin matar aure a cikin shirin firm, wanda malamai suke ta fatawoyi akan sa.
Allah ya karawa Shehu lafiya da nisan kwana, Allah ya saka masa da Alkhairi. Amiin”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

10 Comments

  1. Mutumin da yayi fatawar da a zabi dan izala gwara Christian ai daman bama expecting ya fadi gaskiya a nan. Malamin da yace tasaku yakawo hujjoji amma shehi wani hujja ka kawo??? Allah ya rabamu da son zuciya

      1. Gaskiyane mahaukacine Kai yakamata Ka koma makaranta kaida malamanka mahaukata akwai maganar da hankali kadai ya isa ya aunata bata bukatar Aya don indai Kai ba haukane akanka ba mu tun Kan malamai suyi fatawa mukasan akwai shubuha aciki don Kalmar saki guda dayace.kuma baa wasa da ita Dan wasu ma maganganun kadai na iya kawo Sakin ma Baka sani. Ba kuna zaune kuna auren haramci. Allah katsaremu da imaninmu da hankalin mu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button