Labarai

An Harbe Kwamandan Sojoji Har Lahira A jihar Kastina

’Yan bindiga sun kashe kwamandan sojoji da ake aikin samar da tsaro a wani harin kwanton bauna a yankin Sabon Garin Dan’Ali da ke Jihar Katsina.

Shaidu sun ce a ranar Alhamis ne kwamandan sojojin mai muƙamin Manjo ya gamu da ajalinsa, kuma an kai gawarsa asibiti.

Wata majiya mai tushe ta ce an kai wa sojojin harin ne a kauyen Malali da ke Karamar Hukumar Kankara, inda kwamandan da ya jagoranci kai musu agaji domin kurkushe harin da aka kai wa kauyen.

“Malali yana kan hanyar Zangon Pawwa kuma ka san ’yan bindiga sun mamaye yankin.

“Duk lokacin da aka kai hari jami’an tsaro sukan nemi abokan aikinsu daga sansanin da ke Maraban Dan’Ali su taimaka musu, kuma shi wannan kwamandan yakan amsa ba tare da bata lokaci ba.

“To a wannan karon ma sun nemi hakan, amma sai ya zo a cikin Hilux ba a mota mai sulke ba, watakila ba ta kusa ne a lokacin.

“Sai kuma aka yi rashin sa’a maharan sun bi sawunsa, inda suka harbe shi a kai.”

Wani mazaunin yankin ya ce an yi kazamin fada tsakanin ’yan bindiga da sojojin kafin su dauki gawar kwamandan.

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani daga kakakin sojoji a Jihar Katsina, Oiza Ehinlaidlye, amma hakan bai yiwu ba, saboda jami’in bai amsa kiran ko sakon da wakilin namu ya aika masa ba, har zuwa lokacin da ya aiko rahoton.

Aminiya hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button