Kannywood

A Dalilin Rashin Kwankwaso Ya Sa Zan Zabi Buhari A 2019, Amma A Kano Sai Mun Kada Ganduje, Cewar Nabraska

 
Shahararren jarumin finafinan Hausa Mustapha Nabraska ya bayyana cewa har yanzu yana nan kan akidar Kwankwasiyya.

Nabraska ya bayyana hakan ne biyo bayan wani hoton bidiyo da ya bayyana wanda aka nuno shi tare da Gwamnan jihar Bauchi Barista M.A Abubakar inda yake nuna goyon bayansa game da gwamnatin Buhari.

Game da bidiyon da aka ga jarumin yana tallata APC, Nabraska ya ce “kowa ya san ni dan Kwankwasiyya ne kuma Sanata Kwankwaso ne ubangidana a siyasa. Ya kuma tsaya takarar shugabancin kasa amma Allah ya nufa ba shine dan takara ba, don haka ina da damar da zan iya yin kowane dan takara a sama. 

Duba da yadda nake da iyayen gida a APC irin sun Gwamnan Masari, Gwamna El-rufai, Gwamna M.A Abubakar, Gwamna Bindow, Gwamna Yari da sauransu, wadanda sun san cewa Kwankwasiyya nake yi amma nakan yi musu kara.

To sai na ga tunda ubangida na ya fadi zabe, ya kamata na dauki tafiyar Buhari a sama duba da yadda iyayen gidana bisa karkashin jagorancin Gwamnan Bauchi da Honarabul Dattuwa Ali Kumo suka nemi na koma tafiyar ta Buhari. Wadanda suka kara fahimtar da irin kyawawan manufofin Buhari ga kasa wanda mu da ‘ya’yanmu za su mora.


Sannan ina so jama’a su sani har gobe ina tare da Sanata Kwankwaso. Wannan kawai gudummawa ce zan baiwa Buhari a sama”.

Nabraska ya kara da cewa tafiyar Buharin da ya runguma ba za ta shafi alakarsa da Kwankwaso ba, saboda Kwankwaso tamkar uba yake a gare shi kuma yana da fahimta. Wanda kusan kaf ‘yan siyasan Nijeriya babu mai fahimtarsa.

Nabraska ya ce a sama yake yin APC amma a kasa PDP yake yi domin a Kano ba shi da dan takarar gwamna da zai zaba kamar Kabir Abba Yusuf wanda shine zabin Sanata Kwankwaso. Kuma ba za su kauracewa zabin ubangidansu ba.

Game da ko PDP za ta iya kwatar mulki daga hannun APC, Nabraska ya ce abu ne mai sauki yin hakan duba yadda Abba Kabir Yusuf dan takarar gwamnan Kano na PDP yake kan samun karbuwa a wurin al’ummar Kano saboda zabin Kwankwaso ne.

Game da batun badakalar bidiyon da aka nuna Ganduje yana karbar rashawa, Nabraska ya ce a matsayinsa na dan fim wannna bidiyon gaskiya ne ba na siddabaru bane, amma ba shi da tabbacin kudin rashawa gwamnan yake karba.

Daga Aliyu Ahmad

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button