Kannywood

Shin da Gaske an kori Fatima Mai Zogale daga wajen Aiki?

Fitaccen mawakin wakokin siyasa Adamu Dauda kahutu rarara yayiwa waka wanda ya fitar shekaranjiya mai suna “Fatima mai zogale” wakar tayi dadi sosai.

A jiya ne da dare ake ta yadawa a kafaffen sada zumunta cewa wai uwar gida Fatima mai zogale ta kore ta, ta dalilin wakar da Rarara yayi mata.

To wannan ba gaskiya ne hausaloaded ta samu wani bidiyo inda ita hajiya uwar gida Fatima take bayyani.

“nazo nayi magana akan maganar da ake cewa wai na kori yarinya na akan Rarara yayi mata wakan zogale ni ban taɓa koran yarinya ba, yarinya nan ina zama watan da ya gabata wani ya kawomin ita, tana aiki da wata mata aka kore ta, anka rokeni na dauke ta.

Nace harka zogale nakeyi in zata iya ina da wani waje ‘branch’ da wata yarinya dina to ni bai wuce kwana biyar ba, su kace Rarara yazo ya saje zogale yaci yace zogalen yayi daɗi zai dawo.A jiya ina shagona a gimbiya sleep wajen karfe sha ɗaya 11:pmbtacemin zata bar aiki gobe tana so in biyata, nace mata to dare yayi fati ina zan samu kuɗi in biyaki, kesan kasuwancin nan da kuke zuwa yahuza ba tafiya yake ba tun azumi.

Tacemin ita tafiya zatayi aure ranar juma’a za’a daura mata aure, kuma ina shedanu da yawa da ta gayawa zata je tayi aure ranar juma’a yau da na tashi na je na nemi aron kuɗi na bata, a gaban mutane nace Allah ya baki zama lafiya banda hali da na taimakamiki, saboda keyi aiki dani wata daya zuwa wata biyu.

Yanzu nayi mamaki a soshiyal midiya an sani ana zagina an ce wai na kori fati mai zogale saboda waka.

Ga bidiyon hajiya Aisa nan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button