Ba dole ba ne, wani sai ya taimaki wani a Fim, dan ya talauce ba – Kyauta Dillaliya ta Dadin Kowa
Ba dole ba ne, wani sai ya taimaki wani a Fim, domin kamar aiki ne, ka yi a biya ka, in ji jaruma Kyauta Dillaliya ta shirin Dadin Kowa
Jarumar yar fim din nan Fati Nayo wadda anka fi sani da kyauta dillaliya ta dadin kowa a cikin wata hira da gidan rediyo Freedom Radio Kano inda take mata tambayoyi akan harka fim.
Fati nayo kyauta dillaliya tace mai cewa
” Shugabannin ma basu san masana’atar ba, dukkansu basu san miye masana’atar ba ban fi shekara takwas ba 8 amma nafisu sanin masana’ata kasan miye masana’ata idan kagani zaka iya yimin gaisuwa daso amma sau biyu naganta a rayuwata duk da nake.
Amma tunda muna fim anmin gaisuwa tafi miliyan ita da bintu kaga sau biyu na ganta babu wata alaƙa da ga ganin ƙanwata eh yata shikenan ba wata mu’amala da muke , to misali yan fim da ake cewa basu da hadin kai misali kamar fim kasuwa sabon gari, kasuwa kurmi, kasuwa kwari haka fim yake.
Wani ya talauce baza’a taimaka masa yanzu dan Allah ga tambaya
Tambayata ga yan fim, dan Allah kun taɓa ganin a kasuwa kwari da kasuwa wani ta kare wani ya taimaka masa?
To kasuwa masana’ata haka take , ba wani lallai to ya ankayi anka zama yan uwa, ae ko yan kasuwa ana zama amma ba wanda zai kare a taimakasa, saboda haka mu yan fim ba yan uwa bane, muna dai sana’a ɗaya.- inji kyauta dillaliya
Fati nayo kyauta dillaliya ta kawo misalai sosai akan ba dole bane sai wani dan fim ya taimaka wani dan fim ba a cikin wannan firar ta da Freedom Radio Kano.
Ga bidyon nan ku saurari cikon hirar.