Kannywood

Bazan Iya Fada Da Gwamnati ba A Shirye Nake Na Daina Fim din A Duniya – Tijjani Assase

Bazan Iya Fada Da Gwamnati ba A Shirye Nake Na Daina Fim din A Duniya - Tijjani Assase
Tijjani Assase Mai Shirin Fim Din A Duniya

A CI-gaba da martanin da furodusoshi da daraktocin Kannywood ke yi game da haramcin da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta yi wa finafinai masu nuna kidinafin, shaye-shaye da ƙwacen waya, fitaccen jarumi Tijjani Abdullahi (Asase) ya ce shi idan aka ce ya daina shirya fim ɗin sa mai dogon zango na ‘A Duniya’, to zai daina, domin shi ba zai iya faɗa da gwamnati ba.
Ya ce: “An ce faɗan da ya fi ƙarfin ka sai ka maida shi wasa.”

Idan kun tuna, shugaban hukumar, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), ya faɗa wa mujallar Fim a ranar Talatar nan cewa sun ɗauki wannan matakin ne domin kare mutunci da al’adar mutanen Kano.

Asase na ɗaya daga cikin furodusoshin da ake ganin dokar za ta shafa saboda fim ɗin sa mai suna ‘A Duniya’, wanda ke hasko yadda wasu matasa ke yin harkar daba a Kano.
Duk da haka, jarumin kuma furodusa ya ce abin da ya kamata su Afallah su yi shi ne su yi koyi da Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa, wadda ta bayyana cewa duk mutumin da ya yi laifi a cikin fim, to a nuna sakamakon aikata laifin da ya yi, kada a ba shi mutunci ko girmamawa.
Game da jigon fim ɗin sa, Asase ya faɗa wa mujallar Fim cewa, “Ba wai ina yin fim ɗi na ‘A Duniya’ don shaye-shaye ko daba ba, a’a, akwai wasu ɗabi’u da Allah ya ɗaukaka su a fim ɗin da ɗaukaka darajar fim ɗin, shi ya sa ido ya yi yawa a kan fim ɗin, ake kallon fim ɗin haka.
“Akwai finafinan da ake yin su a kan daba da waye-waye.

Bazan Iya Fada Da Gwamnati ba A Shirye Nake Na Daina Fim din A Duniya - Tijjani Assase
Sanarwar soma haska ‘A Duniya a tashar Africa Magic

“Ni finafinai na ina da saƙo da na ke so na isar kuma ina isar da su a hankali, ina kaiwa ga inda na ke tunani a lissafi na zan kai.
“Kuma a ko da yaushe ina maimaitawa idan aka zo da cewar nan abu kaza bai dace ba, nan abu kaza bai dace ba, zan gyara saboda ba ni da sana’ar da ta wuce ta.
“Idan kuma aka ce ba a so gaba ɗaya, to shi ma zan haƙura. An ce faɗan da ya fi ƙarfin ka sai ka maida shi wasa.
“Ni ba zan yi rigima da gwamnati ba, kuma ba zan ce ban yarda da abin da gwamnati ta ce ba, a’a, face dai ita rayuwar wanda ya yi daidai ya san ya yi daidai, wanda ma bai yi ba ya san ba daidai ya ke aikatawa ba.”
Asase ya ƙara da cewa shi a ko da yaushe kalma ɗaya ce a bakin sa, wato: “Allah ya ba ni ikon yin daidai, kuma Allah ya fahimtar da ni gaskiya, ya kuma ba ni ikon gyarawa.
“Kuma duk mutumin da ya ke magana a kan gyara, gyara, to ni ko da yaushe kamar raƙumi da akala na ke: idan an ja ni a kan gyara, ina tafiya. Allah ya sa hakan da aka yi shi ne mafi alheri a gare ni. Idan ina ɗauko wani nauyi na zunubi aka sauke min, to shi wannan abin taimaka ta ya yi a rayuwa.”

A game da rol ɗin da ta ke takawa a fim, Asase ya yi batanin cewa, “Ni ba hali na ba ne fitowa a ɗan iska, ba hali na ba ne fitowa a ɗan daba, ba hali na ba ne fitowa a mutumin banza, amma fim wannan rol ɗin ya fi ƙarfi a yadda na ke aiwatarwa a cikin fim ɗin.
“Kuma ni mai son gyara ne a ko da yaushe. Ba na goyon bayan ɓarna.
“Kuma shi shugaban Hukumar Tace Finafinai ya faɗa ya ce an yi wannan abin ne don al’umma, don mutanen Jihar Kano. To mu ma mu na yin fim ɗin ne don al’umma, don mutanen Jihar Kano. Idan dai ba a yin haka ba daidai ba ne, to in Allah ya yarda ba za mu yi ba, kuma za mu bi doka don duk wanda ya bi doka shi ne zaman lafiya.”
Duk da haka, jarumin ya yi da cewa ya kamata kafin a ɗau wannan matakin a ce an jira su an zauna da su an tattauna.
Ya ce, “Kamata ya yi a ce kafin a yanke hukuncin, tunda mulki ne na siyasa, sai a kirawo mu a ce, ‘To ga matsalolin da ba ma so, ga kuma yadda mu ke so a dinga yi, ga yadda ya dace a zama; idan ka ga za ka iya yi sai ka ci gaba da yi, idan kuma ba za ka iya ba sai ka haƙura’.

“Amma kuma kamar ina ganin ba komai ba ne, misali ka fito ka ce dole sai an yi shawara da kai idan za a yi wani hukunci tunda ni ba dokar ƙasa na sani ba, ban san yadda dokar ta ke ba, don haka ba zan ce ya zama wajibi dole sai an kira mu ba kafin a yanke hukunci ba. Zan iya tabbatar da hakan daidai ne ko ba haka ba ne?

Bazan Iya Fada Da Gwamnati ba A Shirye Nake Na Daina Fim din A Duniya - Tijjani Assase
Fostar shirin ‘A Duniya’ wanda ake nuna shi a YouTube

“Kawai dai shi wanda ya yi ya san hakan shi ne daidai. Kuma in ba a yi wasa ba, ba shi kaɗai ya yanke ba, kamar ya yi shawara ne ko kuma a gwamnatance ko majalisa ce ta zauna ta zartas da shi ta saka shi a cikin doka tunda ita dokar da ta ke riƙe da hukumar ai majalisa ce ta yi dokar, don haka ka ga shi ma za a ba shi dokar ya karanta ne, kuma ba sai an yi shawara da mu ba.”
Shi dai Asase, likkafar sa ta yi gaba, domin fim kuwa za a fara nuna ɗin sa mai dogon zango na ‘A Duniya’ a tashar talbijin ta Africa Magic Hausa da ke kan satalayit ɗin DSTV da na GoTV daga ranar 1 ga Oktoba, 2021.
Mun dauko wannan rahoto daga fimmagazine

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button