Ya kamata Gwamnatin Kano ta waiwayi kauyuka maimakon gina gadoji a birni – Naziru Sarkin waka
Shahararren mawakin nan Naziru m Ahmed wanda anka fi sani da Sarkin waka san kano yayi fira da gidan jaridar Dclhausa inda ya bada shawara ga gwamnatin jihar kano da ya kamata raya kauyuka domin suma suna da hakki a cikin gwamnati ba iya yan birni ba kawai.
Naziru sarkin waka yayi firar ne a cikin wani faifan bidiyo inda yake mai cewa.
“Ni tunda Rabiu musa Kwankwaso yazo yayi gadoji wannan alhamdullahi, ganduje shima yazo ya kara akwai na yaba masa musamman ta wajen kwarin nan ta ɗan rage cinkoso a nawa ganin duk ba wani fita nake sosai ba.amma yanzu gwamnan kano ya kamata ya mayar muna da hankali akan tituna da suke cikin unguwani da layuka, sa’an akwai wani abu da nake dauka a matsayin kuskure amma su ban san miye na su ba.
Wani lokacin nake gani kamar wani dan zalunci zalunci, misali kudin karamar hukumar musamman kudin ƙiru a shigo da su cikin kano ace za’a yi aiki da shi, mutanen ƙiru a barsu ba aiki ko a shigo da kudin kura ace za’a yi aiki da su, duka wadanda aiki gwamoni da sunka zo a waje biyu zuwa ukku suke yin su bai wuce kumbuso, municipal, fage , dala sai nasarawa biyar kenan duk a wannan wajen nan ne ake jifge kuɗin jihar kano.
Idan muna fira da yan kwangila sai kaji sunce ankawo fayin din ruwa nan sai yayi shekara nawa ba’a iya zuwa a ƙara yi musu aikin nan ba, muna ganin su ana nuna basu da ruwa ba su da wuta, ba su da ilimi makarantun su , ya kamata a kula akan abubuwan da suke da shi, tun da gwamnatin tarayya tana bada kuɗin na su na karamar hukuma.
Sai kuma gyaran asibitoci da anka fara kudin pension na wadanda mutane gajiyayo na yaba masa.- inji naziru sarkin waka.