Hirar Aminu Saira Daraktan Labarina, akan Cigaban Shirin Labarina Season 4
A cikin wannan hira da ankayi da babban daraktan shirya fina finai kuma shine daraktan labarina mai dogon zango wanda ankayi hirar da shi a wajen da suke aikin cigaban shirin na hudu da na biyar a turance season 3 and season 5 kuma ya bayyana ranar da za’a dawo da haska season 4.
Aminu saira ya bayyana labarina an fara shi tun cikin shekara 2014 zuwa 2015 wanda shahararren marubuci ibrahim birnewa ya rubuta shi kadai daga zango na farko zuwa na biyu ,yayinda sauran anka shigo da sababbin marubuta.
Aminu saira ya sha tsangwama da gulma a gefe ana cewa kamar bashi da hankali shi da yake masu gutun zango ina zai kai mai dogon zango.
Malam aminu saira ya bayyana babban abinda yafi burgeshi akan labarina shine yadda mutane yara da manya suke kallon shirin labarina kamar da gaske wanda yace akwai har furofesas da suke kiransa suna mansa martani akan shirin fim din wanda yace hakan yana matukar burgeshi.
Ga cikakken bayyani nan a cikin faifan bidiyo.