Labarai

Kwanan nan mutum 300,000 da su ka kammala shirin N-Power za su samu bashi da ga CBN — Minista

Kwanan nan mutum 300,000 da su ka kammala shirin N-Power za su samu bashi da ga CBN -- MinistaGwamnatin Taraiya ta baiyana cewa waɗanda su ka amfana da shirin N-Power 300,000 ne za su bashi da ga Babban Bankin Nijeriya, CBN bayan sun ɗauki horon koya sana’o’i.
Ministar Ayyukan Jin ƙai, kula da afkuwar ibtila’i da Ci gaban Al’umma, Sadiya Umar Farouk ce ta baiyana hakan a yau Alhamis yayin taron manema labarai na ministoci na mako-mako da ma’aikatan yaɗa labarai na fadar shugaban ƙasa ke shirya wa.
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito ministar na cewa akwai wani tsari na waɗanda za su kammala shirin, wanda a kaa yi shi bisa hadin gwiwa da Babban Bankin Nijeriya, CBN.
Ta ƙara da cewa da ga cikin mutum 500,000, 300,000 ne su ka nuna sha’awar yin shirin kammalawa inda za a yi musu horon kan sana’o’in hannu, sannan a basu bashi da ga CBN a matsayin jari na su fara yin sana’a.
Ministar ta ce tuni shiri yayi nisa kuma ana tsaka da shirye-shirye na fara horas da waɗanda su kara nuna sha’awar su, inda ta baiyana kwarin gwgiwar cewa kafin karshen zangon farko na shekarar da mu ke ciki, CBN za ataa raba musu wannan bashi na kuɗi.
Ta yi bayani cewa ma’aikatar ta ba ta bada bashi sai dai ta yi haɗin gwiwa da ma’aikatun da su ke harkokin bada lamuni.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button