Labarai

Kotu ta sanya 3 ga Maris a matsayin ranar da Abduljabbar zai bada bayanan kariya

Kotu ta sanya 3 ga Maris a matsayin ranar da Abduljabbar zai bada bayanan kariya
A yau Alhamis ne Babbar Kotun Shari’a da ke zamanta a cikin birnin Kano ta sanya ranar 3 ga watan Maris a matsayin ranar da Malamin Addinin nan, Abduljabbar Nasiru Kabara zai bada bayanan kariya
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a na ci gaba da Shari’ar Abduljabbar ne bayan da a ke zargin sa da yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammadu (Tsira da Amincin Allah su Tabbata a Gare shi).
A’a na zargin Abduljabbar ne dai da Laifuka 4 da su ka shafi yin kalaman ɓatanci ga Ma’aiki.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Sarki Ibrahim Yola ne ya sanya ranar bayan da lauyan Abduljabbar, Ambali Obomeileh-Muhammad, SAN ya roki kotun da ta ɗage zaman domin a baiwa wanda ya ke karewa damar yin bayanan kariya.
Shi ne sai Sarki Yola ya ɗage zaman sai ranar 3 ga Maris domin ci gaba da sauraron ƙarar.
A ranar 3 ga Fabrairu ne dai kotun ta baiwa Gwamnatin Kano da ta kira shaida na ɗaya domin tuhuma.
A ci gaba da shari’ar a yau, lauyan gwamnati, Suraj Sa’eda, ya zo da shaida na ɗaya, PW1, Adamu Adamu, inda bayan ya gama yi wa Abduljabbar tambayoyi ne, shi ne kotu ta sallame shi ta kuma sanya 3 ga watan Maris domin wanda a ke ƙarar ya kare kansa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button