Labarai

Hukuncin zaben kano: shiri ne da yunkurin rusa arewa da alummanta- Dr. Idris Ahmad

Advertisment

Dr idris ahmad wani mutum daya fito daga arewa maso gabas a jihar yobe wanda Allah ya albarkaci shi da zama kasar ingila inda a can ne yake aikin wanda masaniya sosai akan harka tsaro da kariya ta tsaro a harkat yanar gizo, mutum ne wanda yake harkat kire kiren motoci a kasar ingila inda yayi tsokaci akan Shari’a da anka yanke a kotun sauraren kararaki tsakanin mai girma gwamna Engr.Abba kabir Yusuf da kuma Dr. Nasiru yusuf gawuna.

Assalamu Alaikum Jama’a barkanmu da wannan lokacin. Ina son nayi takaitaccen tsokaci game da abinda ya faru a Kano jiya. Wallahi wannan ba harkan siyasa irin wadda aka sani bane. Jama’a idan mun zurfafa tunani zamu fahimci cewa wannan wani yunkurin ne makiyanmu suka shirya na rusa tsarin siyasan Arewa, da kuma rusa Arewa da Al’ummanta.

Wadanda suka shirya wannan danyen hukuncin a Kotu jiya sune suka yi yunkurin hadamu yaki da Yan’uwanmu a Jumhurriyar Nijar. Alhamdulillah, Allah Ya lalata bakar anniyarsu. Toh gashi yanzu suna son su hada mummunan husuma a tsakanin Al’ummanmu a Jihar Kano.

A cikin kwanaki 100 kacal, mai girma Gwamna Engineer Abba Kabir Yusuf ya seta Jihar Kano akan tsari mai inganci irin na zamani, yadda Al’umma zata sami kwanciyan hankali, arziki da walwala. Azzaluman shugabannin Najeriya sun fahimci cewa idan suka kyale Abba ya ci gaba da irin wannan mulkin, toh ba Kano ba, Arewa gaba daya zata gyaru. Saboda haka gwara su dakile Abba kafin tafiyan tayi nisa.

Advertisment

Saboda haka, Jama’a sai muyi hattara, musamman matasanmu. Dole ne mu kiyaye duk wani abu da zai kawo fitina da tashin hankali. Kada kowa ya karya doka. Kada kowa ya fita yin zanga-zanga, ko kone-konen kadara, ballantana yiwa yan’uwanmu rauni. Yin hakan ya zama rashin hankali mai tsanani.

Matasanmu da ke Jihar Kano mu nuna wa makiyanmu da azzaluman shugabannin Najeriya cewa mun fisu wayo, basira, da hangan nesa. Mu nuna musu cewa don sun ingizamu ta bayan fage, ba zanu illata juna ba. Mu nuna musu cewa don rai ya baci hankali ba zai gushe ba. Kano ita ce cibiyar Arewa. Sobada haka Insha Allah ba zamu yarda Kano ta shiga hargitsi ba.

Daga karshe, Jama’a ina kara tunatar da mu akan mu ci gaba da yin Istighfari, addu’a, Al-Qunut da tallafawa marasa galihu a tsakaninmu. Insha Allah, babu abinda zamu gani bayan wannan sai Alheri.

Na barku lafiya.

Dr. Idris Ahmed.
Coventry, UK.
21/09/2023.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button