Budurwa Mai Shekara 31 a Duniya Ta Fito Neman Saurayi Ruwa Ajallo
Wata budurwa a TikTok ta ce ta gaji da zama marar aure, domin haka ta bayyana sha’awar samun soyayya ta gaskiya.
Kyakkyawar budurwar mai amfani da sunan Nafisafjf a TikTok, ta sanya bidiyoyi da dama inda take gaya wa mutane yadda kaɗaici ke ci mata tuwo a ƙwarya.
Nafisafjf ta ce ta shagaltu da yin aiki da gina sana’ar ta wanda hakan ya sanya ba ta da lokacin yin wata soyayya.jaridar legit na ruwaito.
Amma yanzu, bayan ta kai shekara 31 a duniya, budurwar ta ce ta gaji haka nan da tafka kuskuren da ta yi a baya, inda yanzu take son samun wanda za su yi soyayya tare.
Nafisafjf ta ce ta gaji da zama babu aure kuma ta ce a shirye take ta yi maraba da duk wanda ya nuna ra’ayin soyayya da ita ta hanyar tura mata saƙo.
Ta rubuta akan TikTok cewa:
“Na shagaltu da sana’ata har na kai shekara 31 ni kaɗai. Na gaji da zama marar aure. Wataƙila kana son turamin saƙo, akwai lamba ta a cikin bio.”
Ƴan soshiyal midiya sun yi martani a karkashin bidiyo dinta.
@ugboesotuvalentin ya rubuta:
“Kina buƙatar soyayya, ba abokin tarayya ba, ki sami wani sojan ruwa. idan kina da hali mai kyau ko kina cikin aiki za ki samu wanda zai so ki.”
@Bademosi A.J ya rubuta:
“Kyakkyawa kamar ki za ki samu wanda zai zama rabin ranki nan ba da daɗewa ba.”
@Alfred ya rubuta:
“Ina fatan za ki duba yiwuwar ƙarɓa ta?”
@eagle1 ya rubuta cewa :
Kina da kyau
Amma ina tantama idan bakida abokin zama a halin yanzu.