Labarai

EFCC ta kama tsohon Ministan Sufurin Jiragen Saman Nijeriya hadi sirika

EFCC ta ce nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da Sirika tare da ɗan’uwansa Abubakar a gaban kotu kan zargin almundahanar N8.06 bn.

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon-ƙasa (EFCC) ta ce ta kama tsohon Ministan Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika bisa zargin almundahana.

Shugaban hukumar EFCC Ola Olukoyede ne ya tabbatar da hakan ranar Talata a ganawar da ya yi da manema labarai a Abuja.

Ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za su gurfanar da Sirika tare da ɗan’uwansa Abubakar a gaban kotu kan zargin almundahanar N8.06 bn.

Rahotanni sun ce zargin da ake yi wa tsohon ministan yana da alaƙa da yadda ya tafiyar da batun ƙaddamar da jirgin saman Nijeriya, wato Nigeria Air da kuma sauran batutuwa.

TRT AFRIKA HAUSA

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button