Kannywood

Martanin Falalu Dorayi akan Maganar Ladin cima kan Biyanta kudin Fim

Falalu dorayiBayan irin kalamai da jaruma ladin cima tayi akan cewa ana biyanta naira dubu biyu ko biyar wanda ba’a taba bada naira dubu talatin ko hamsin ba. Ya sanya jarida bbhausa da ta dauki nauyi wajen kawo daga bakin mai ita.
Shine shafin bbchausa sun ruwaito falalu dorayi yayi martani akan ta ga abinda yake cewa.

Falalu Ɗorayi yana daga cikin manyan daraktoci a Kannywood kuma yana daga cikin daraktocin da ke saka Ladin Cima a cikin fim. A cewarsa, ya yi mamaki dangane da kalaman Ladin Cima inda ya ce tun da yake sa ta a fina-finai, bai taɓa biyan ta ƙasa da dubu ashirin ba inda ya ce yana biyanta talatin zuwa arba’in.

“Ba a yi kwana goma ba na yi aiki da ita kuma abin da na bata shi ne naira dubu talatin,” in ji shi.

Ya bayyana cewa a girma irin na Ladin Cima da yadda ake kallonta a matsayin kaka a Kannywood babu wanda zai biya ta hakan idan ba yara ƙanana waɗanda suke tasowa ba.

Falalu Ɗorayi ya bayyana cewa bai taɓa samun matsala da ita ba “hasali ma haka kawai ta kan kira ni ta ce wane ya ba ni kuɗi ta yi mani godiya ta kuma ce na kira shi na yi mashi godiya”, in ji shi.

Ya ce haka kawai idan mutum ya yi mata alkhairi tana kiransa ma ta faɗa masa inda kuma ya ce a lokacin da ta samu matsalar muhalli ta samu kuɗi daga wurin ƴan Kannywood sun fi miliyan guda.

Ya bayyana cewa ko a fim ɗin Gidan Badamasi ta yi masa sin biyar inda ya biya ta dubu araba’in.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button