Mansurah Isah : Zamu dauki mataki akan ki, idan baki Janye kalamanki ba – Gwamnatin kano
Gwamnatin Jihar Kano ta buƙaci tsohuwar ƴar wasan Kannywood Mansurah Isah ta janye kalaman da ta yi a wani bidiyo wanda ta yi zargin ana maɗigo a wata makarantar gwamnati a Kano.
Kwamishinan Ilimi na Kano Umar Haruna Doguwa ne ya tabbatar wa TRT Afrika da hakan a wata tattaunawa inda ya ce sun yi iya bincike sun gano abubuwan da Mansurar ta faɗa ba gaskiya ba ne.
Hukumomin jihar ciki har da Ma’aikatar Ilimi da hukumar Hisbah sun ce ko dai Mansura ta yi wani bidiyon ta janye kalamanta tare da ba da haƙuri, ko kuma a ɗauki mataki a kanta.
“Wannan magana ba wai ta gwamnati ba ce, ta al’ada da addinin mutanen Kano. Muna so ta zo ta yi bidiyo ta janye kalamanta ta ba da haƙuri, to kuma mu ɗauki matakin da ya dace.
A kwanakin baya ne dai tsohuwar ƴar wasan ta yi wani bidiyo inda take zargin akwai wata makarantar gwamnati a Kano inda yara ƴan kimanin shekara bakwai ke da ƙungiyar maɗigo.
Bayan haka ne hukumar Hisbah da haɗin gwiwar Ma’aikatar Ilimi suka ɗunguma domin bincikar makarantar, inda har aka tashi tawaga ta je makarantar ta ɗauki ɗaliban da ake zargi da madigon zuwa asibiti domin yi musu gwaji.
Kwamishinan ilimin ya ce an shafe tun daga safiya har zuwa dare ana binciken yaran a asibiti amma daga ƙarshe likita bai gano wata hujja da ke nuna cewa ana lalata ko maɗigo da yaran amma ba a samu ba.
Kwamishinan ya ce hasali ma bayanai da suka samu daga wurin abokan Mansurar sun nuna cewa ta ƙirƙiri wannan lamari ne domin ta samu kuɗi.
Kwamishinan ya ce sun bai wa Mansura dama ta janye kalaman nata idan ba haka za su ɗauki mataki a kanta.
Ita ma mataimakiyar Kwamandan Hisbah Dr Khadija Sagir a hirarta da TRT Afrika, ta jaddada cewa “Duk bincikenmu ya nuna babu wannan zargi da Mansura ta yi. Don haka muna so Mansura Isah ta yi bidiyo ta janye maganarta saboda jama’a sun shiga damuwa. ”
Sai dai a martanin da Mansurar ta mayar a wata hira da ta yi da gidan rediyon Freedom Kano, ta ce ba za ta iya janye maganar da ta yi ba saboda gaskiya ta faɗa.
Ta kuma bayyana cewa abin da ta yi ba laifi bane sakamakon tana aiki ne da ƙungiya mai zaman kanta kuma ta yi haka ne domin jawo hankalin hukumomi da kuma iyayeyn yara su ƙara sa ido kan abin da ke faruwa.
TRT AFRIKA HAUSA