Kannywood

RAHMA SADAU: Jan Hankali Mai Muhimmanci Ga Mata Masu Yada Tsiraicinsu ~ Falalu Dorayi

Yin barna ko yada ta kowacce iri ce bana goyan bayanta. Lallai shigar tsiraici ga mace musulma, sharri ne mai girma gare ta, da kuma al’ummar da take cikinsu. Kuma shigar zubar da mutuncin zuri’ar ta ne.
Rashin magana akan wannan yana daidai da kace a cigaba da aikatawa. Ita kuma ukubar Allah in ta tashi zuwa za ta shafi kowa ne. Allah ya shirye mu.
Nasiha da jan hankali ba da tozarci ba ita ce hanya mafi kyau musulmi ya yi wa dan uwansa musulmi nasiha, akan wata barna da ya ga yana aikatawa.
Ita dai dabi’ar shigar banza nema take ta zama ruwan dare ga al’ummarmu. Abu ne
da yake faruwa a rayuwar yau da kullum, mu duba gidajen biki, gidan suna, tarurruka, makarantun mu tun daga primary za ka ga wasu yara mata na tafiya kansu babu dankwali sai gashin kansu a daure, ballantana aje secondary ko Universities, Duk wadannan suna faruwa a gaban IYAYE, MALAMAI, YAYYE, KAWUNNAI.
Mace tana da daraja gyaruwarta gyaruwar Al’umma ne, mu tashi tsaye akan nusar dasu kunyar su da mutunci su. Domin gyaran ‘Yayanmu masu zuwa a gaba.
Rasulullah Annabi (S.A.W) Yace”Dukkaninku masu kiwo ne, kuma kowannenku za a tambaye shi game da abin da aka bashi kiwo”.
Kofar tuba a bude take da duk wanda yai kuskure, gaggawar Istighfari yafi Jinkirin yinsa.
Dukkan mu masu laifi ne, Allah ne yake rufa namu asirin.
A cigaba da addu’ar neman gafarar Allah
A KARSHE
Ga Hadisin Annabin tsaira (S.A.W) akan masu FIDDA TSIRAICI
Yace;
“A karshen zamani za’a samu wasu mata ga tufafi a jikinsu amma tsurara suke, tufafin bai rufe tsiraicin suba.”
RASULULLAH (SAW) Yace;
“A TSINE musu, domin su din TSINANNUNE.” RASULULLAH (SAW) Yace; “Wallahi ko Kamshin ALJANNA baza su ji ba.”
Allah ka shiryamu da zuriarmu da dukkan musulmi baki daya.
Wajibine Mazan da Matan mu tashi mu yaki Shaidan La’anannen Allah, Yadda baibar Uban Talikai Annabi Adamu ba, haka muma bazai bar mu ba. Yakinsa kullum shine yasa mu kauce hanyar Allah mubi tasa batacciya.
Allah ya shiryemu baki daya ya tsare mu biyewa son zuciyarmu. Amin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button