Kannywood

Nasiha da wa’azi ya kamata malamai su baiwa yan fim ba zagi ba – Daushe

Jarumin fina finan Hausa na Kannywood Rabiu Muhammadu wanda aka fi sani da Daushe a wata hira da ya yi da manema labarai ya bukaci malaman addini cewa a maimakon kudin goro da suke yi wa masu harkar fim a matsayin mutanen banza.

Su dinga fitowa suna bai wa masu harkar fim shawarwarin da ya kamata su dauka domin ci gaba da gudanar da harkar cikin aminci da tsoron Allah, ba duka ne aka taru aka zama daya ba kamar yadda wasu suke tsammani dole akwai na kwarai da kuma na banza a cikinmu in ji Daushe.

Nasiha da wa'azi ya kamata malamai su baiwa yan fim ba zagi ba  - Daushe
Daushe

Jarumin barkwancin ya kara da cewa ba gaskiya bane maganar da ake cewa jaruman fim basa taimakawa ‘yan uwansu jarumai a lokacin da suke bukatar taimako musamman na rashin lafiya ko kuncin rayuwa, inda ya ce ana yi masu wannan kallo ne saboda komai nasu a kan idon Duniya suke yi ba kamar sauran al’umma ba.

Ba jaruman fim kadai ne suke da kasawa a wajen taimaka wa ‘yan uwan sana’arsu ba,a kowace mu’amala ko zamantakewa dole ne ka samu wadanda suke taimako da wadanda basa yi,amma saboda mu komai akan idon Duniya muke yinsa hakan yasa ake kallon kamar mu kadai ne a haka in ji Daushe.

-leadership hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button