Rashin Imani : Matsahi ya bankawa Mutane Wuta Suna Sallar Asuba A Masallaci a Kano
Ana tsaka da Sallar Asuba a safiyar Laraba a masallacin ne mutumin ya zuba musu fetur ya kyasta wuta sannan ya kulle su a ciki
Shaidu sun ce ana tsaka da Sallar Asuba a safiyar Laraba a masallacin ne mutumin ya shigo ya rurrufe kofofin ya zuba fetur ya kyasta wuta sannan ya kulle su a ciki ya tsere.
“Da kyar mutanen da suke waje suka yi nasarar balle kofar su ceto na cikin masallacin,” in ji wani mazaunin yankin.
Aminiya ta samu bayani cewa akalla mutane 28 ne suka samu mummunan kuna a sakamakon wutar da mutumin ya cimma a masallacin fa ke unguwar A adawa da ka Karamar Hukumar Gazawa ta jihar.
Wakilinmu ya ruwaito cewa an kai mutanen da suka kone asibiti domin ba su kulawa a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke birnin Kano.
Majiyoyi a yankin sun ce kimanin mutane 40 ne suke sallar a masallacin a lokacin da mutumin ya yi wannan aika-aika.
Aminiya