Labarai

Ba zamu yafewa wanda ya banka mana wuta muna Sallah ba cewar Wadanda aka kona

Mutum 13 ne suka rasu wanda aka bankawa wuta a Masallaci suna Sallar Asubah.

Matshin da ya cinna wuta a masallaci rahotank da suke fitowa na cewa kaza kaza ne ,Sai dai wakilin rahama tv ya bayyana cewa kididigar da hukumar asibiti ta bada sanarwa mutum 9 ne Allah ya karbi ransu.

Matashi Shafi’u Abubakar matashin da yayi fani da man fetur ya banka wa masallata wuta suna sallah asuba gidan rediyo Rahama tv ya samu zantawa da wasu da suke iya samun magana inda suke cewa.

Idris Marwanu daya daga cikin wanda iftila’in ya shafa yana mai cewa, eh haka naji ana fadi cewa tsokana shi naji fadin cewa ake akan an raba gado bai aminta ba.

“Shidai haka yake fada kuma ba gaskiya bane, sai shi rigimar rabon gado shine kan gaba, an raba gadon dai-dai wai shi yace bai yarda ba, da limami da wansa ne sunka raba gadon- inji idris marwanu

Malam idris Marwanu yacigaba da cewa ” gaskiya bamu ji dadi ba kuma bamu yafe ba, nidai ban yafe masa ba wallahi , in duk gaba daya mutane sun yafe nidai ban yafe ba, tunda ba hakkina a wajen- inji malam idris Marwanu .

Sauran mutane da na jikita da yan uwansu sunyi Allah wadai da Allah yasa kamar yadda zakuji daga bakin su

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA