[Bidiyo] ladin cima haruna: Sarkin Waka yayiwa Ali Nuhu Da falalu dorayi kacha kacha
Inda shine darkata ali nuhu yayi tsokaci da nuna rashin jindadinsa inda yake cewa
“Ka san wasu suna yi wa jama’a yadda suka ga dama ne, wani sai ka ga ya kyautata maka wani kuma ka ga bai kyautata maka ba.
“Ya kamata idan mutum yana bayani ya rinƙa bambancewa ya ce wasu suna kyautata mana ya kuma ce wasu ba su yi ,” in ji Ali Nuhu.
Ali Nuhu ya ce kalaman da Ladin Cima ta yi sun ja masa zagi sosai a wurin jama’a domin fim ɗin baya-bayan nan da tayi tare ta yi da shi.
Wanda shima darakta falalu dorayi ya fadi albarkacin bakinsa game da maganar ladin cima inda yake cewa.
“Ba a yi kwana goma ba na yi aiki da ita kuma abin da na bata shi ne naira dubu talatin,” in ji shi.
To shine sarkin waka nazir m ahmad ya fito cikin bacin rai ya nuna cewa wallahi babu Allah a zukatansu yace abinda tsohuwar nan ta fadi tabbas haka ake basu inda yace Ali nuhu da falalu dorayi kuji tsoron Allah ku fadi gaskiya,sarkin waka nazir m ahmad ya fito yayi rantsuwa da Allah anyiwa tsofaffin nan haka a masana’antar kannywood nazir m ahamd yayi maganganu masu yawa cikin bidiyonsa mai minti shida.
Ga bidiyon nan kasa ku saurara.
https://youtu.be/OpHrbhC5jaY
One Comment