Kannywood

Iftila’in da ya faru da tsohuwar jaruma Maryam Wazeery “Lailah labarina” da Mijinta

Tsohuwar jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maryam Musa Waziri wadda ke amsa sunan Laila Masu Gonar Naira a tsohon shirin Labarina Series da ya gabata, ta gamu da mummunar hatsarin mota a hanyar Kaduna zuwa Zariya tare da mijinta, Tijjani Babangida wadda tsohon dan wasan kwallon kafar Najeriya ne, da d’an ta Muhammad Fadeel da kuma kanin mijinta, Ibrahim Babangida a ranar Alhamis.

Kanin mijinta, Ibrahim Babangida, shi ya ke tuka motar da su ke ciki lokacin da hatsarin ya faru, wadda kuma a take Allah Ya karbi rayuwar sa, in da aka garzaya da ita kuma Maryam da d’anta da mijinta zuwa Asibiti don kula da lafiyar su.

Iftila'in da ya faru da tsohuwar jaruma Maryam Wazeery "Lailah labarina" da Mijinta
Kanin Ibrahim Babangida wanda ya rasu

Majiyarmu ta Nagudu TV ta ruwaito cewa, sai dai kwana daya da hatsarin (wato a daren jiya kenan) Allah Ya yi wa karamin d’an na ta, Fadeel rasuwa shima sakamakon buguwar da ya yi.

A yanzu haka dai a cikin mutum 4 da su ka yi hatsarin, Maryam da mijinta ne su ka saura, in da su ke karbar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika a Zariya.

Daga cikin abun da wannan hatsari ya jawowa tsohuwar tauraruwa Maryam Waziri shine rasa bangare daya na fuskar ta:

Iftila'in da ya faru da tsohuwar jaruma Maryam Wazeery "Lailah labarina" da Mijinta
Maryam, Babangida suna kwance a asibiti, Ɗan su ya rasu

Ta rasa ido daya
Ta rasa kunne daya
Bangaren hancin ta ya gutsire
Gefen bakin ta ma ya gutsire

Da fatan Allah Ya jikan Ibrahim da Fadeel, Ya gafarta musu. Ya bawa Maryam da Tijjani Babangida lafiya. Amin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button