Labarai

Harin Masallaci: Mutum 7 sun rasu da matashi ya cinnawa wuta a kano

Mutanen da suka rasu a wutar da ake zargin wani matashi ya cinna wa masallaci a jihar Kano sun ƙaru zuwa takwas.

Da safiyar jiya Laraba rundunar ƴansandan jihar ta ce ta kama Shafi’u Abubakar mai shekara 38 da ake zargin ya kunna wa masallacin wuta lokacin da mutane fiye da 30 ke sallar Asuba a ciki.

Lamarin ya faru ne a garin Gadan na ƙaramar hukumar Gezawa.

Daga bisani, bayan da Mataimakin Sifeton Ƴansanda na Shirya ta Ɗaya, Umar Sanda ya kai ziyara ga wadanda abin ya shafa da ke kwance a asibitin Murtala, ya ce mutum daya ya rasu, 23 kuma sun jikkata.

Sai dai kuma wani mazaunin ƙauyen mai suna Hamisu Abdullahi ya faɗa wa BBC Hausa cewa mutum takwas ne aka tabbatar da mutuwarsu zuwa yammacin yau Laraba.

“Yanzu haka an kawo gawar mutum bakwai da muka yi wa jana’iza, ɗayan kuma sai gobe da safe za a binne shi,” in ji shi yana mai cewa ɗaya daga cikinsu ɗan’uwansa ne.

Ya ƙara da cewa “waɗanda suka rage a asibitin za su kai kamar 22”.

‘Yan sanda sun ce mutumin ya yi amfani da bam ɗin da aka haɗa da man fetur, inda mutum 24 duka maza suka ji raunuka, 20 daga cikinsu manya da kuma yara huɗu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button