Jarumi Adam A Zango Ya Bayyana Kudin da Ya kashe a Fim dinsa Na ” Gwaska Return”
Na kashe miliyan 12 kan fim din gwaska – Inji Adam A. Zango
Fim din Gwaska action fim ne, wanda akwai fada da wasan tashi a cikinsa, irin fina-finan nan ne da ake kira super-hero films, wato jarumi mai ceto al’umma
A hirarsa da ‘yan jarida, Adamu Zango, ya ce, sai da fim din Gwaska ya lashe masa miliyan 12, kuma a hakan bai ma gama kashewa ba tukun.
Fim din Gwaska action fim ne, wanda akwai fada da wasan tashi a cikinsa, irin fina-finan nan ne da ake kira super-hero films, wato jarumi mai ceto al’umma, fim din zai fito a badi a watan maris.
Za’a fara bude fim din a silima da ma a wuraren da ake tsammani kamar manyan shaguna, kuma a cewar masu shirin fim din, abun ya kayatar.
An dai ga jarumai da yawa, a wurin, an kuma ga tsohuwar masoyiyarsa wato Nafisata Abdullahi.