Kannywood

Martani: Ganduje Bai isa ya Rushemin Gida Ba – Rarara

Fitaccen mawakin siyasar nan a Najeriya dama wajen ta Dauda Kahutu Rarara ya bayyanawa duniya wasu abubuwa dangane da takaddamar sa da Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Mawakin yace ko gidan sa akan layin lantarki yayi yasan Ganduje ba zai rushe masa ba sai dai idan wani zai gina masa.Martani: Ganduje Bai isa ya Rushemin Gida Ba - Rarara

Domin gidan sa Gwamnati ce ta gina sa shi kawai abunda yayi shine kara sabunta shi.

Haka kuma ya kara da cewa a shekarun baya lokacin zabe Sak da akayi ita ta haifar da Sakarkaru da ake ta fama dasu yanzu haka.

Ya kuma cewa ko “ya”yan Ganduje baza su nuna masa kusanci dashi ba sannan da hidimar da yayiwa Ganduje illa mutum daya,wanda yayiwa laqabi da yayansa wato Sulen Garo.

Ga bidiyon nan ku saurara

 

Haka kuma ya bayyana wasu mawaka da suke neman inda gineginen sa da kadarorin sa suke domin su sa a talauta shi.

Sai dai mawakin bai bayyana sunan mawakan biyu daya fada a fakaice ba.

Ba tare da bata lokaci ba zaku iya kallon cikakken bidiyon anan kasa.

Kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button