Labarai

A karon farko mace ta bugu kirji za ta jagoranci zanga-zanga kan kisan da ake yi wa ‘yan Arewa a Abuja

A karon farko mace ta bugu kirji za ta jagoranci zanga-zanga kan kisan da ake yi wa ‘yan Arewa a AbujaZainab Ahmad wacce aka fi sani da Bint Hijazi ta fito ta bugu kirji inda ta ce za ta jagoranci zanga-zanga a yau Juma’a 12 ga watan Disambar shekarar 2021 a babban birnin tarayya Abuja, kan kisan kiyashin da ake yiwa al’ummar Arewa amma gwamnati tana nuna halin ko in kula.
A wata hira da tayi da fitaccen dan jaridar nan ma’aikacin gidan jaridar DW, wato Nasiru Adamu El-Hikaya, Zainab ta bayyana bacin ranta a fili, inda ta ce tunda ta ga cewa abin ba na kare bane, ya kamata ta sadaukar da rayuwarta domin ceto al’ummar Arewa.

Bint Hijazi ta ce abinda ta kasa ganewa shine, ‘yan Arewa an mayar da su bayi ne, ko kuwa rayukan su ba a dauke su a bakin komai bane, inda ta ce yadda ake kashe mutane a Arewa ko kaji ba a yiwa irin wannan kisan wulakancin.
Ta ce duk wannan abu da yake faruwa a Arewa babu wanda yake fitowa yana magana, daga ‘yan jarida, Malamai, ‘yan siyasa da sauran su duka babu wanda yake magana akan wannan abu, sai Bint Hijazi ta bayyana cewa Malam Bello Yabo ya nuna zai goyi bayanta wajen gabatar da wannan zanga-zanga, inda ta ce ya bayyana cewa zai fito wannan zanga-zanga da za a gabatar a yau.
Jaridar Labarunhausa na ruwaito cewa ta ce a yau Juma’ar nan za su fita, kuma za su gindayawa gwamnati bukatu, inda ta ce a cikin bukatun za su nemi gwamnati ta tura sojojin sama dana kasa suje inda wadannan mutane suke, tunda an riga an san inda suke a cikin dazukan.
Zainab ta ce babu maganar ace yau anje an kashe ‘yan bindiga a nan gobe a wancan wuri, inda ta ce suna so ayi wannan abu a cikin ‘yan kwanaki a gama kowa ya huta, domin kuwa wulakancin da ake yiwa al’umma ya yi yawa.
Ta ce ran dan Kudu daya aka taba, amma gwamnati ta dauki mataki ta kuma bayyana cewa za ta yi maganin wadanda suka yi wannan abu, amma a Arewa kullum sai an kashe daruruwan mutane, amma babu wanda ya nuna halin in kula.

Ta ce har wani bidiyo aka aika mata, inda aka nuno gonaki ana watsa musu fetir ana banka musu wuta, inda ta ce hakan alamu ne kawai dake nuni da cewa ana so a karar da yankin Arewa.
Ta ce tabbas akwai wani abu a kasa, ana so ne kawai a karar da yankin Arewa ya zama ‘yan Arewa sun koma kame-kame na wajen da za su zauna.
Ta ce wannan zanga-zanga da za ayi ba a ware kowa ba, ta ce zanga-zanga ce da ta shafi duk wani mutum dan Arewa kuma mai kishin Arewa, tafiya ce da ta shafi duk wani wanda yake ganin yana cikin kunci a yankin Arewa, tafiya ce ta kowa da kowa babu wanda aka ware a ciki.
Ta ce a kowacce jiha akwai shugabanni da suka nuna goyon baya wajen wannan zanga-zanga, saboda haka kowa zai dauki jama’ar shi za su bayyana inda za su hadu. Inda ta ce a bangaren ta kuma a birnin Abuja, a yau da misalin karfe 8 na safe za su fito. Zainab ta ce ita ta dauki wannan abu a matsayin jihadi, dan haka bata damu ba idan har sun fito sun kashe su, ko sun kama su.
Ta ce za su fara tafiyar daga Unity Fountain, inda za su dangana har zuwa fadar shugaban kasa, domin kai masa kukan halin da yankin Arewa ke ciki.

A karshe Zainab ta yi kira ga ‘yan jaridu na gida Najeriya dama na kasashen ketare da su fito su bada goyon baya don tabbatar da cewa sun dauki duk wani abu da ake yi a wajen wannan zanga-zanga, inda ta ce zanga-zanga ce ta lumana, don haka baza a bari wani ya tada hankali ko ya jawo abinda zai zama matsala ba a wajen.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button