Labarai

Bidiyo : Allah Sarki!! Dan Allah Kalli Wani Sabon Abin mamaki Da Gwamna Zulum yayiwa Talakawa

Mai Girma Gwamna, Babagana Umara Zulum a safiyar yau Lahadi ya katse ziyarar aiki da ya kai birnin tarayya Abuja inda ya dawo Maiduguri, daga nan ya dauki jirgin mai saukar angulu na soji domin ziyartar al’ummomin da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai wa hari da yammacin jiya Asabar, a karamar hukumar Hawul da ke kudancin jihar.
Gwamna Zulum, ya bar birnin Maiduguri zuwa jihar Katsina da Abuja a ranar Alhamis, domin gudanar da wasu ayyuka, ya katse ziyarar bayan harin ta’addancin.
garuruwa hudu ne yan ta’adda suka kaiwa hari a ranar Asabar data gabata wanda suka da, Tashan Alade, Shafa, Azare, Sabon-Kasuwa da Debro inda maharan suka lalata makarantu, kantuna da wuraren ibada. Bayan harin an tabbatar da kashe mutane uku a garin Shafa, biyu daga cikin su mafarauta ne da farar hula ‘daya. Dubban buhunan kayan amfanin gona da manoma suka girba kwanan nan na daga cikin abunda maharan suka sace shaguna adana kaya da shagunan bakin kasuwa.
A garin Yimirshika, Azare, Sabon-Kasuwa da Shafa Gwamna Zulum ya duba irin tarin duniya da aka lalata sannan ya ba da umarnin sake gina wuraren da aka kona ba tare da bata lokaci ba wadanda suka hada da ofishin ‘yan sanda, rumfunan kasuwa da sauran su.
A garin Shafa, Gwamna Zulum ya ba da umarnin samar da motocin sintiri guda shida da sauran kayan aiki don kara karfafa tsaro a tsakanin al’umma. Haka zalika a garin Yamirshika Gwamnan ya bada umarnin samar da motocin aiki ga mafarauta da kuma ‘yan banga.
Gwamna Zulum ya yi jawabi ga mazauna garuruwan da suka firgita suka dawo garin Yamirshika a jiya Asabar, bayan da masu tayar da kayar baya suka yi kokarin kai musu hari inda aka dakile harin na su.
“Mun ta so daga Abuja zuwa Maiduguri da safiyar yau, kuma mun zo nan ne don nuna alhinin mu da kuma tsayawa gare ku, ‘yan uwan mu da dake karamar hukumar Hauwal, game da abin da ya faru na bakin ciki a jiya. An yi min cikakken bayani kuma na ga abubuwa da idanu na, insha’Allah, zamu karfafa tsaro a nan da kuma duk sauran wuraren. Ba tare da bata lokaci ba zamu biya mu ku da dukkanin bukatun ku kamar yadda muka tattauna da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro da shugabannin ku. Zamu gyara ofishin ‘yan sanda, kantuna da duk sauran kayayyakin more rayuwa da aka lalata jiya ”In ji Gwaman Zulum.
Gwamna Zulum yace nayi matukar kaduwa bayan hare-haren saboda kare rayuka da dukiyoyin su shi ne ginshikin gwamnati.
“Kamar yadda yake kunshe cikin sashe na 14, 2b a kundin tsarin mulkin Nigeria na shekarar 1999, tsare rayuka da dukiyoyi al’umma shine babban ginshikin kowace gwamnati, mun san wannan kuma muna yin duk iya abun da zamu iya don samar da tsaro da kuma tabbatar da jin dadin ‘yan kasa. Ba za mu kauce wa nauyin da ke kan mu ba, za mu ci gaba da jajircewa tare da mai da hankali wajen neman zaman lafiya a Borno ”In ji Gwaman Zulum.
A ganawar shi da manema labarai Gwamnan ya ce ya kawo ziyarar ne domin karfawa al’ummomin da kuma bayar da kayan aiki ga matasa yan sa kai da ke tallafawa jami’an tsaro wajen maido da zaman lafiya.
Tawagar da suka rufawa Gwamnan baya wajen yin jajen ta hada da Mataimakin gwamna Umar Usman Kadafur, tsohon mataimakin gwamna Usman Mamman Durkwa, sanata mai wakiltar Kudancin Borno, Mohammed Ali Ndume, komishinan ma’aikatar sake ginawa tare da tsugunar da yan gudun hijira Engr. Mustapha Gubio da kuma komishinan ma’aikataraikin gona da albarkatun kasa, Engr Bukar Talba.
Voice of Borno.
https://youtu.be/aT8IAXe2lEc

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button