Labarai

Sojin saman Nijeriya sun musanta sakin bam ga masu Mauludi a Kaduna

A cikin wata sanarwa da safiyar Litinin, sojojin sun ce sa’o’i 24 da suka gabata, ba su kai wani samame ta sama a shacin jihar Kaduna ba.

Sojojin a sanarwar da Daraktan yada labarai Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar, ta ce ya kamata mutane su san cewa ba sojojin sama kadai ke samame a jirage ba a arewacin Nijeriya.

Majiyarmu ta Dclhausa na ruwaito,Sanarwar ta kara jan hankalin ‘yan jarida da su rika tabbatar da sahihancin labari kafin su buga.

Jaridar Daily Trust dai ta wallafa cewa ana zargin jirgin sojin saman Nijeriya ya saki bam ga wasu mutane da ke bikin Mauludi a kauyen Tudun Biri na karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, inda rahotanni suka ce hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 30 ko sama da haka.

Wani labari na daban : Yawan amfani da wayar salula na sa karancin maniyyi a jikin Dan’adam – Binciken masana

Yawan amfani da wayar salula na taimakawa wajen kawo karancin ruwan maniyyi a jikin Dan’adam kamar yadda binciken masana a kasar Switzerland ya gano.

Binciken ya gano cewa matasa maza masu shekaru 18-22 da ke amfani da wayar salula sau 20 a rana, na a sahun gaba wajen haduwa da wannan hatsarin na karancin ruwan maniyyi.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button