LabaraiUncategorized

Duk iskancin yan matan Tiktok sai kaga ana aurenau mu masu hijabi an Kyalemu – Arewa Queen

Duk iskancin yan matan Tiktok sai kaga ana aurenau mu masu hijabi an Kyalemu - Arewa QueenGaskiya ana yaɗa baɗala a Tiktok sai kaga Yarinya Bahaushiya ta saka Bum short ko mini skirt da crop top cibiya a waje tana rausaya da kada jiki.
Kuma duk da iskancin nan ba zai hana kaga an zagaya an aure su ba mu a bar mu da Hijabi tunda iyayen suna da Ya’yan banki.
Wata matashiya ce mai suna Arewa Queen, da alama kuma yar jihar Kaduna ce kuma mazauniyar birnin zazzau, ita ce take bayyana haka a kafar facebook.
A dukkan alamu tana mayar da martani ne kan irin yadda yan mata musamman na hausawa suke yawan taammali da kafar Tiktok suna nuna tsaraici, da raye-raye, waɗan su ma sun mayar da kafar wajen zage-zage.
A saboda haka ne ma matashiyar Arewa Queen, take cewa zaa iya kyale su duk da su masu hijabi, ne a aje a auri Yan matan Tiktok duk da irin tabargazar da suke yi.
Abun tambayar a nan shine, shin da gaske ana kyale masu hijabi aje a auri Yan matan Tiktok masu yin rawa da riguna waɗanda basu rufe cibiya ba?
DAGA Shuaibu AbdullahiMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button