Labarai

Buhari bai dauki rayukan ‘Yan Arewa a bakin komai ba, sai gantali da yawon banza ya sani – Aisha Yesufu

A wani bidiyo da fitacciyar ‘yar gwagwarmayar nan, kuma daya daga cikin wadanda suka samar da kungiyar “BringBackOurGirls”, wato Aisha Yesufu, ta nuna bacin ranta matuka dangane da halin ko in kula da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake nunawa dangane da rayukan al’umma da ake kashewa a kasar musamman ma a Arewacin Najeriya.

Jaridar Labarunhausa ta ruwaito Aisha ta ce ta san ba wai yanzu aka saba zagin ta ba a duk lokacin da ta fito ta caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma a wannan karon dole ta fito tayi magana, inda ta ce, lokacin da tsohon shugaban kasar mulkin farar hula, Shehu Shagari, ya rasu shugaban kasar bai je wajen jana’iza ba.

Ta cigaba da cewa haka a lokacin da Kanal Abu Ali ya rasu a filin daga, a lokacin da yake kokarin ganin ya kare rayukan al’umma, mutane daga kowanne sassa na kasar nan sunyi gangami don zuwa wajen jana’izar shi, amma shugaban kasar yana Abuja cikin Villa, bai fito ya halarci jana’izar sa ba.

Fitacciyar ‘yar gwagwarmayar ta ce, idan tafiyar banza ce ko taron siyasa a wannan lokacin ne za ka ga shugaban kasar yana rawar jiki, amma duk wani abu da ya shafi talaka babu ruwan shi a ciki, musamman ma idan aka ce a yankin Arewa ne.

Aisha Yesufu
Aisha Yesufu – Source: Twitter

Aisha ta ce akwai wani bidiyo da ta taba yi a shekarar 2019, wanda mutane suka yi ta faman zagin ta a kanshi, a lokacin da shubaban kasa yaje jihar Zamfara, ta ce har ya gama ziyarar shi bai yiwa mutanen jihar jaje kan iftila’in da ya afka musu a wancan lokacin ba.
‘Yar gwagwarmayar ta ce duka ‘ya’yansa a yanzu babu wani wanda yake da matsala, domin kuwa duka ya riga ya saita su, ya kuma saita kanshi da duka iyalansa, yanzu talaka ne kawai yake shan bakar wahala.

Aisha ta ce akalla ita a wannan lokacin za ta iya sayen abinci ta ci tayi bacci, amma akwai miliyoyin mutane da babu cin yau babu na gobe, ga bala’in tashin hankali da suke ciki, mutane na zaune lafiya lau za a zo a far musu da harbi a kashe na kashewa a yanka na yankawa ayi gaba, kuma babu abinda zai faru.
Ta ce ba zai yiwu mutane kawai su zauna su ce iya addu’a kawai za su yi ba, domin kuwa ko Annabi Muhammad SAW ba a Masallaci kawai ya zauna baa, ya fita ya nemawa kanshi da addinin shi hakki a lokacin da ya shiga kunci, saboda ta yi kira ga al’ummar kowacce jiha da su tashi tsaye, su fita su gabatar da zanga-zanga domin nunawa duniya da shugabanni cewa abubuwan da ake yi ya isa haka.
Aisha ta ce yanzu idan wani ya fito ya fito daga wani yankin na Arewa ya ce yana son shugabancin kasa, da wane baki za su yi magana, domin kuwa a yanzu wanda suka bawa goyon baya, dan Arewa ya gaza yi musu komai, ya bari ana kashe su kamar dabbobi.
Aisha ta ce wannan abu ba wai abu bane na siyasa, abu ne da ake maganar rayukan al’umma, inda ta bada misali da mutanen da aka kashe a Sokoto ‘yan kwanakin nan, ta ce akwai yiwuwar a cikin su akwai wadanda suka dangwalawa shugaban kasar kuri’unsu.

Ga dai bidiyon, da kuma abinda take cewa daga bakin ta:

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button