Labarai

Kada Ka Yiwa Bazawara Wadannan Abubuwan Idan Kana Soyayya Da Ita

Zaurawa sun kashi kusan kashi uku. Ko wacce da yadda ake tinkaranta da soyayyar neman auren ta.
Akwai zaurawan da ake yiwa lakabi da sauta ga wawa. Irin wadannan zaurawan basu wuce watanni a gidan miji ba auren su yake mutuwa, suma soyayya da su daban yake.

Akwai zaurawan da mazan su suka mutu ko a sanadiyar ciwo ko hadari. Suma dabarun tinkaransu daban. Akwai zaurawa da aka rabu dasu aka bar su da yara, suma soyayya da su ba daya bane da sauran. Akwai zaurawa da sun jima gidan aure aka sako ko bari basu taba yi ba.

Kada Ka Yiwa Bazawara Wadannan Abubuwan Idan Kana Soyayya Da Ita
Kada Ka Yiwa Bazawara Wadannan Abubuwan Idan Kana Soyayya Da Ita

Wadannan sune kadan daga cikin jerin zaurawan da yanzu haka suke kusan gidajen uban kowa. Kai taka wacce iri ce?
Zauran da suke da aka sako su da yara a gabansu sune suka fi yawa kuma sune mafi yawan maza suke soyayya dasu.

Irin wadannan zaurawan kada ka sake ka ce baka son abun da suka haifa amma kana sonsu. Muddin ka nuna wa yaranta kiyayya to ka rasa soyayan ta.

Irin wadannan zaurawan basu son karya ko yaudara. Ka fito ka tsaye ka fadamusu gaskiyar abunda kake so ko kake yi. Muddin suka fahimci ka makaryaci ne zaka iya rasa soyauarsu.

Wadannan zaurawan sun tsani takura da bibiyan harkokinsu. Idan kana cikin mazan da suke yawan takurawa mace da jin kwakwaf. To kana iya rasa soyayya su.

Mata ne da basu so ka raba su da abunda suke yi ko suka saba yi. Muddin zaka yi kokarin raba ta da wasu harkokin ta data saba yi to kuma iya yin hannun riga da ita.

WWadannan sune manyan abubuwan da irin wadannan zaurawan suka tsana ga duk namijin dake soyayya dasu. Kai taka wacce irin bazawara ce mu gaya maka sirrin mallakan ta.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button