Labarai
Ana barazanar daina kai tumatur daga arewacin Najeriya zuwa kudu


Kungiyar dillalan tumatir da hadaddiyar kungiyar masu safarar kayan abinci da dabbobi ta Nijeriya, na barazanar daina kai tumatir a jihar Lagos.
Hakan ya biyo bayan zargin wulakanta musu kaya da suka ce ana yi.
Alhaji Ahmad Alaramma, shugaban kungiyar dillalan tumatir din ne ya sanar da hakan a taron manema labarai da suka kira a Zaria jihar Kaduna.
Ya ce lamarin da ya faru a kasuwar Oke-Odo a jihar Lagos ya jaza an lalata musu ‘kiret’ kusan 60,000 na tumatir, saukin ma, babu tumatir din a ciki.
Majiyarmu ta samu labarin daga Dclhausa cewa, ya ce ana sayar da kowane ‘kiret’ daya na tumatir a kan kudi N6,000, da yanzu haka mambobin kungiyar sun yi asarar kudin da suka kai N360m.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





