Labarai
Fitacciyar Jarumar Nollywood ta musulunta bayan ta auri musulmi
Advertisment
Fitacciyar jarumar fina-finan turanci na Kudancin Najeriya (Nollywood) Mo Bimpe ta sauya addini daga Kiristanci zuwa musulunci bayan ta auri abokin aikinta, Jarumi Adedimeji Lateef.
Hausadailytumes sun ruwaito angonta, wanda shima fitaccen jarumi ne a masana’antar Nollywood ya tabbatar da hakan a shafin sa na Instagram.
Jarumin ya kuma bayyana cewa, amaryarsa ta sauya suna zuwa Rahimullah Adebimpe.
View this post on Instagram
Advertisment
Ma’auratan sun samu saƙonni sama da 10,000 wanda akasarin su na yabo ne da taya murna daga masoyansu da ke bibiyan shafin su na Instagram da kuma abokan aikin su.