Labarai

Tarihin Rayuwar Marigayi Abba Kyari

Advertisment

An haifi Malam Abba Kyari, wanda dan kabilar Kanuri ne, a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Ya yi karatun firamare da sakandare a jihar ta Borno, amma ya yi digirinsa na farko a Jami’ar Warwick da ke Ingila a fannin halayyar dan Adam, wato Sociology a 1980.

Kazalika ya sake kammala wani digirin a fannin Shari’a a Jami’ar Cambridge.

A shekarar 1983, ya zama lauya bayan ya halarci makarantar koyar da aikin lauya ta Najeriya, wato Nigerian Law School.

Advertisment

A shekarar 1984, ya kammala digirinsa na biyu a fannin Sharia’a daga Jami’ar Cambridge.

Daga bisani ya halarci Kwalejin Gudanarwa ta Lausanne da ke Switzerland a 1992, kuma ya halarci horo a kan Gudanarwa da Ci Gaban al’umma a Makarantar Koyon Kasuwanci ta Harvard a 1994.

Marigayi Abba Kyari, ya yi aiki a wurare da dama, wadanda suka hada da Editan New Africa Holdings Limited Kaduna daga 1988 zuwa 1990.

A 1990, ya zama Kwamishinan Gandun daji da albarkatun dabbobi na jihar Borno.

Daga 1990 zuwa 1995, Kyari ya rike mukamin sakataren kwamitin gudanarwa na African International Bank Limited, wani reshe na Bankin bayar da rance da kasuwanci.

Kyari ya taba zama darakta a Bankin United Bank for Africa, inda daga bisani ya zama shugaban bankin.

A 2002, an nada shi a matsayin darakta a Unilever Nigeria, kuma ya taba aiki a Exxon Mobil Nigeria.

Yadda coronavirus ta shiga fadar shugaban Najeriya
Kusoshin gwamnati da suka kamu da coronavirus a Najeriya
Yaya tsarin aikinsa yake?

Abba Kyari shi ne shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa
A matsayinsa na shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Malam Abba Kyara yana da ruwa da tsaki a kan kusan komai da ya shafi shugaban kasar.

Shi ne mutumin da yake tsara komai game da ayyukan shugaban kasar, sannan yakan gana da akalla mutum 20 a kowacce rana, a cewar wasu ma’aikatan fadar ta shugaban Najeriya.

Wani dan jarida da ke dauko rahotanni a fadar shugaban Najeriya, wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya shaida wa BBC cewa a kullum Abba Kyari yana gana wa da Shugaba Buhari akalla sau hudu.

Kazalika yana ganawa da gwamnoni da ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati wadanda ke son gana wa da shugaban kasa.

A fannin siyasa, a shekarar 2015 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar.

Wannan mukami ya ba shi cikakken iko lamarin da ya sanya shi a idanun jama’a, inda ake zargi yana juya akalar gwamnati da kuma zarginsa da cin hanci da rashawa.

Alal misali, a watan Satumbar 2018, Fadar shugaban Najeriya ta wanke Malam Abba Kyari daga zargin rashawa.

Jaridar Punch da ake wallafawa a kasar ce ta buga labarin da ya ce Malam Abba Kyari ya karbi hanci na N29m domin ya bai wa wani mutum kwangilar sayo motocin da za a rika amfani da su a fadar shugaban kasar.

Shi kansa Shugaba Buhari ya taba fitowa fili yana cewa babu wanda yake juya akalar gwamnatinsa.

Yana da mata daya, wacce suruka ce ga marigayi Talban Bauchi, Ibrahim Tahir inda suke da ‘ya’ya hudu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button