Yan Boko Haram suka sace daliban Greenfield ba yan bindiga ba ~ Sheikh Ahmad Gumi
Babban malamin addini, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa yan ta’addan Boko Haram ne suka sace daliban Greenfield dake Kaduna ba yan bindiga ba.
An yi garkuwa da daliban ne a ranar 20 ga watan Afrilu 2021, a makarantarsu dake Kaduna.
Tun lokacin aka yanke cewa yan bindiga masu garkuwa da mutane ne suka sace yaran.
Amma a ranar Talata, Sheikh Ahmad Gumi a hirarsa na AIT ya bayyana cewa bincike ya nuna yan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa da yaran.
Kamar yadda Legit na ruwaito.Yayinda aka tambayeshi shin yana da tabbacin yan Boko Haram ne, yace: “Tabbas kam. Yayinda muka yi kokarin bibiyansu domin yi musu magana, wanda muka tuntuba wanda shi ma Fulani ne sun yi masa barazana.”
“Sun ce idan ya cigaba da damunsu zasu kamashi kuma shi kansa sai ya biya kudin fansa kafin a sake shi.”
“Kuma shugabansu dan Jalingo ne. Ba irin Fulanin da muke dasu a nan bane. Saboda haka akwai matsalar rikicin Arewa maso gabas a nan kuma ya kamata muyi gaggawa. Bamu da lokaci.”
Boko Haram Kidnapped the Greenfield University Students, not Bandits – Sheikh Gumi pic.twitter.com/4v1a2TjW2g
— AIT (@AIT_Online) May 4, 2021