Kannywood

Kalaman Rarara : masoyin buhari ya maka masoyin rarara kotu

Bayan kalaman rarara akan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi shekaranjiya ya tayar da kura a Najeriya shine masoyan ko wane bangare sun samu husuma har takai su kotu kamar yadda MD mai amfani da kafar sada zumunta.

Kalaman Rarara ga Buhari sun haifar da rikic! mai zafi a tsakanin masoyin Rarara da masoyin Buhari a jihar Kaduna.

Kalaman suka da mawaki Dauda Adamu Abdullahi Rarara yayi ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari sun haifar da zazzafar rikicinci a tsakanin wani masoyin Buhari da masoyin mawaki Rarara a jihar Kaduna.

Tun da fari dai, wani masoyin Buhari mai suna Mika’ilu Shehu Idris ne ya zag! mawaki Rarara a sakamakon sukar da Rarara ya yiwa tsohon shugaban kasa Buhari a wani taron manema labarai da Rarara ya gabatar a wannan mako.Kalaman Rarara : masoyin buhari ya maka masoyin rarara kotu

Lamarin da bai yiwa masoyin mawaki Rarara Aliyu Hashimu dadi ba, kuma zazzafar rikici ta barke a tsakanin masoyin Buhari da masoyin mawaki Rarara, inda masoyin Rarara wato Aliyu Hashimu ya lakadawa masoyin Buhari wato Mika’ilu Shehu Idris dukan kawo wuka.Kalaman Rarara : masoyin buhari ya maka masoyin rarara kotu

Shedun gani da ido, sun tabbatar da cewa sun yi iya kokarin su don sasanta rikici anma lamarin ya cutura har sai da masoyin Mawaki Rarara wato Aliyu Hashimu ya lakadawa masoyin Buhari kashi.

Yanzu haka dai masoyin Buhari wato Mika’ilu Shehu Idris, ya garzaya babbar kotun shari’a dake Kawo a jihar Kaduna don neman hakkin sa bisa dukan kawo wuka da Aliyu Hashimu masoyin Rarara yayi masa a gaban jama’a.Kalaman Rarara : masoyin buhari ya maka masoyin rarara kotuMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button