Labarai

Barayin daji sun kashe wata mata saboda ta ki yadda su yi zina da ita a Katsina

Wani magidanci mai suna Malam Aminu Yusuf, mazaunin garin Jibia a jihar Katsina ya zayyana yadda barayin dajin da suka dauki matar sa Mai suna Malama Ladi suka kashe ta daga baya bayan ta ki amincewa su yi zina da ita a daji.

Kamar yadda majiyarmu ta samu daga jaridar Leadership na ruwaito, Malam Aminu Yusuf ya zayyana yadda lamarin ya afku tun daga sace ta daga gidan sa har zuwa kashe ta din bayan sun hada kudin fansa sun kai ma su.

Barayin daji sun kashe wata mata saboda ta ki yadda su yi zina da ita a Katsina
Barayin daji sun kashe wata mata saboda ta ki yadda su yi zina da ita a Katsina

Ya ce a satin da ya gabata ne dai yan bindigar suka shigo garin na Jibia kuma suka sace wasu mutane ciki hadda matar ta sa. Sai dai ya ce daga baya sun cigaba da magana da barayin wadanda suka bukaci ya ba su Naira miliyan 10 kafin daga bisani ya rago kudin zuwa Naira miliyan 2 amma da kyar ya samu ya tattara Naira dubu dari bakwai

(N700,000) bayan ya saida motar sa da wasu kadarorin sa.
Sai dai Malam ya ce hankalin sa ya tashi sosai lokacin da ya ji magana na yawo a gari ta bakin wata matar daban da yan bindigar suka sako cewar an kashe matar ta sa wanda kuma daga bisani yan bindigar da suka sace matar ta sa suka tabbatar masa da hakan.

A cikin wani faifan sauti da ya rika yawo a kafafen sadarwar zamani, an ji dan bindigar yana tabbatar ma da Malam Aminu Yusuf mutuwar matar ta sa inda yace wani yaron sa ne ya ce yana son ta da aure kuma har ma ya kawo goro amma da ya matsa yana so yayi zina da ita ta ki yadda ta ce sai dai ya kashe ta, shi kuma ya harbe ta da bindiga.

Malam Aminu Yusuf dai ya ce yanzu ba ya iya yin bacci ma saboda tashin hankalin da yake ciki musamman na rashin matar ta sa da kuma kananan ya’yan da ta bar masa ciki hadda dan shekara ɗaya dake shan nono yanzu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button