Shin Da Gaske Ali Nuhu Tallafawa Da Fatima Naira Miliyan 2 ?
Sakamakon rashin samun kyakkyawar kulawa ta hanyar yin aiki yadda ya kamata ya sa an garzayo da Fatima zuwa wani Asibiti dake Abuja daga Sokoto domin sake yanke wani sashe na kafarta.
Fatima wadda yanzu haka an shigo da ita Abuja, za a kara yanka wani sashen kafar na ta ne zuwa saman gwaiwar ta, kamar yadda rahotanni suka nuna, kasancewar aikin da aka yi mata a farko ba haka ya kamata ya kasance ba, wanda idan ba a yanke din ba zai iya jawo mata damuwa.
Idan ba a manta ba dai, Fatima ta gamu da tsautsayin yanke mata kafa ne sakamakon taka da wani dan makarantar su ya yi a yayin bikin kammala jarabawa a Sokoto.
Tun a farko dai Fatima Sulaiman ta soma jinya ne a asibitin UDUTH dake jihar Sokoto, kafin daga bisani aka garzayo da ita zuwa Abuja.
A gefe daya kuma yayan Fatima ya tabbatarwa da RARIYA cewa batun jita-jitar da ake yadawa cewa fitaccen jarumin finafinan Hausa, Ali Nuhu ya bada gudummawar naira milyan biyu domin jinyar kanwar tasa, ba gaskiya bane, labari ne mara makama bare tushe. Don haka ne ya yi kira da jama’a da su yi watsi da wannan jita-jitar.
KARANTA WANI LABARI
Mutumin Da Ya Yi Kwanaki 16 Yana Tattaki Daga Birmin Kebbi Zuwa Abuja Domin Taya Buhari Murnar Cin Zaben 2015, Yana Cikin Kuncin Rayuwa, Domin Yanzu Haka Ba Shi Da Cin Yau Bare Na Gobe
Mutumin mai suna Malam Haruna Alpah Bazabarme, ya ce ya yi nadamar zaben Buhari da kuma tattakin da ya yi, kuma yanzu haka tsawon shekaru uku kenan da jarin sana’ar sa ta gwanjo ya karye amma babu yadda zai yi.
To kalubale gare ku mukarraban shugaba Buhari, domin ya kamata su waiwayi wannan Dattijo domin tada masa komada.